Kannywood

Duniya Sabuwa : Za mu riƙa ba furodusoshi jiragen ƙasa kyauta don su shirya finafinai, inji Amaechi

Za mu riƙa ba furodusoshi jiragen ƙasa kyauta don su shirya finafinai, inji AmaechiMINISTAN Sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya yi alƙawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta riƙa bayar da jiragen ƙasa da tashoshin jiragen ga furodusoshi domin su riƙa shirya finafinan su.
Haka kuma ya yi kira a gare su da su riƙa shirya finafinai masu inganci da za a iya gogawa da su a ko’ina a duniya, domin yin hakan zai taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin Nijeriya.
Amaechi ya bada wannan tabbacin ne a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban kamfanin shirya finafinai na Native Media, Mista Rogers Ofime, da abokan aikin sa, waɗanda su ka kai masa ziyarar godiya saboda izinin da ya ba su na shirya fim ɗin su mai suna ‘Conversations in Transit’ da jiragen ƙasa da tashoshin jiragen.
A jawabin sa, ministan ya nanata ƙudirin sa na tallafa wa furodusoshi a duk lokacin da su ka buƙaci a ba su aron jirage da tashoshi domin ɗaukar fim.
Ya ce za a ba su waɗannan kaya da wurare ne ba tare da sun biya ko kwabo ba don a taimaka masu wajen shirya finafinan su.
Amaechi ya yi alƙawarin zai ci gaba da tallafawa wajen ɗaukar fim ɗin ‘Conversations in Transit’ da ma duk wani fim da za a yi.
Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta kyakkyawan kallon da ake wa ƙasar nan.

Duniya Sabuwa : Za mu riƙa ba furodusoshi jiragen ƙasa kyauta don su shirya finafinai, inji Amaechi
Rahama sadau a wajen daukar shirin fim din conversation in transit

A cewar sa, ya bada amincewar a shirya fim ɗin a jirgin ƙasa da tashoshin jirgin ne domin a nuna wa duniya irin ingantattun kayan aiki na zamani da cigaban da Nijeriya ta ke samu a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce: “Tilas mu yi hakan saboda a nuna wa duniya abin da shugaban ƙasa ke yi a ɓangaren samar da kayan aiki.
“Shugaban ƙasa ya inganta kayan aiki kuma reluwe ya na ɗaya daga cikin su. Dole ne mu ba su wannan damar su yi amfani da jirgin saboda duniya ta san cewar mu na cika alƙawuran da mu ka yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.”

Mista Rotimi Amaechi (a hagu) tare da Rogers Ofime a lokacin ziyarar

Ministan ya ƙara da cewa bai wa mashirya fim ɗin amincewar su yi amfani da jirgin wajen shirya fim ba tare da sun biya ko kwabo ba wata gudunmawa ce da gwamnati ta bayar domin haɓaka wannan masana’antar.
Ya ce, “Za mu ci gaba da inganta kayayyakin aikin mu domin mu haɓaka cigaban al’ummar mu. Hanyoyin mota da reluwe su na cikin muhimman kayan aiki, don ko da ka ƙera abu to ka na buƙatar kyawawan hanyoyi.
“Aikin shirya fim ɗin tunani ne mai kyau; zai ba mutane abin yi mai ma’ana, kuma ya samar da nishaɗi sannan ya haɓaka tattalin arzikin mu.
Mu na jin daɗin su na yin shi kuma hakan ne ya sa za mu kasance a shirye a ko da yaushe mu ba su amincewar su yi amfani da jirgin a duk lokacin da su ke buƙatar yin amfani da shi.
“Ya kamata masu shirya fim su inganta abin da su ke yi. Inganta ko me ka ke yi ya na da muhimmanci. Sun ci gaba da haɓaka a tsawon lokaci.
“Ingantuwa domin ka zarce kowa a duniya ba wani abu ba ne mai wahala. Za su iya zarce kowa a duniya idan akwai sadaukar da kai sosai.”
A nasa jawabin, shugaban kamfanin Native Media, Mista Ofime, ya gode wa Amaechi saboda amincewar da ya ba ta su yi amfani da jirgi da tashoshin a kyauta don shirya fim ɗin su na ‘Conversations in Transit’.
Ofime ya ce ya yi tunanin shirya fim ɗin ne sakamakon abin da ya gani lokacin da ya shiga jirgin ƙasa a daga Legas zuwa Ibadan, wanda ya ce abin ya burge shi matuƙa
Ya ce: “Lokacin da na zo Nijeriya daga ƙasar Kanada, abin da ya fi burge ni matuƙa shi ne tafiyar da na yi a jirgin ƙasa daga Legas zuwa Ibadan kuma wannan ɗin ya sa na yanke shawarar shirya fim ɗin.

Rogers Ofime da ma’aikata a lokacin ɗaukar ‘Conversations in Transit’ a tashar jirgin ƙasa ta Legas
Rogers Ofime da ma’aikata a lokacin ɗaukar ‘Conversations in Transit’ a tashar jirgin ƙasa ta Legas

“Na ɗaya ina so in nuna nasarar da gwamnati ta samu sannan kuma in sanar da mutane cewa akwai wata hanyar ta daban ta sufuri wadda ta ke da ban-mamaki sosai.
“Mutane su na ta shiga jirgi kuma abin da su ke faɗi ya na da daɗin ji sosai.”
Ofime ya ce fim ɗin ‘Conversations in Transit’ labari ne na zamani wanda ke nuna tsagwaron soyayya da kuma barkwanci, wanda ke nuna wa mai kallo rayuwar wasu ma’aurata miji da mata har gida uku waɗanda su ke fama da batun mutuwar aure, neman sabuwar soyayya da kuma wani ƙullin soyayya mai wuyar warwarewa.
Ya yi nuni da cewa shi ne fim na farko a industirin fim ta Nijeriya wanda aka shirya shi kacokam a cikin jirgin ƙasa.
Ofime ya ce Native Media kamfanin shirye-shiryen talbijin ne wanda ya ci kyaututtukan karramawa a baya, kuma ya shekara 10 da kafawa, sannan ya ciri tuta wajen shirya finafinai masu inganci da aka gina a kan tantagaryar labaran asali na Afrika don nuna wa masu kallon talbijin waɗanda buƙatun su ke ci gaba da sauyawa.

Duniya Sabuwa : Za mu riƙa ba furodusoshi jiragen ƙasa kyauta don su shirya finafinai, inji Amaechi
Raham sadau da uzee usman wajen daukar shirin conversation in transit

Mujallar Fim ta ruwaito cewa jaruman Kannywood Rahama Sadau da Uzee Usman su ne jaruman fim ɗin na ‘Conversations in Transit’.
(Fim magazine)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button