Labarai

Talauci yayi sanadiyar yankewa karamar yarinya yar shekara 13 hannu a zamfara

An yankewa wata yarinya ƴar shekara 13 hannu mai suna Fauziyya Sani sakamakon rashin kuɗin kai ta asibiti a jihar Zamfara

Matuƙar kana raye ba a gama halittar ka ba har sai ka koma ga Allah, Comr Nura Siniya wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta ya wallafa labarin.Talauci yayi sanadiyar yankewa karamar yarinya yar shekara 13 hannu a zamfara

wannan yarinyar da kuke gani sunan ta “Fauziyya Sani, ta haɗu da tsautsayi a satin da ya gabata sakamakon faɗowa da tayi daga kan gado wanda hakan yasa ta samu karaya a hannu wanda sanadiyyar haka ne yasa aka gutsure mata hannu sakamakon rashin kuɗi da iyayenta suke fama dashi a jihar Zamfara.

A zantawar da gidan talabijin na yanar gizo Mai-Biredi Tv suka yi da Fauziyya ta bayyana cewa tun farko ɗaurin gida ne da aka yi mata wanda hakan yai sanadiyar riƙe mata jijiyoyin hannu wanda yasa jini baya motsawa.Talauci yayi sanadiyar yankewa karamar yarinya yar shekara 13 hannu a zamfara

A cewar Fauziyya ta kammala karatunta na firamare tsawon shekara 3 da ta wuce amma har yanzu bata samu damar cigaba da karatu ba saboda rashin kuɗi har bayan faruwar wannan jarabawar da Allah yai mata, inda tace tana son ta cigaba da karatu idan ta samu wanda zai taimaka mata.

“Koda wannan abun ya same ni da ƙa
yar muke iya samun abinci”

“Burina inaso na ci-gaba da karatu domin na zamo likita- fauziya_fauziyya”

Ga bidiyon ku saurara abin tausayi.

Allah Ya raba mu da mummunar ƙaddara ya bata ikon cinye wannan jarabawar ya kuma bata lafiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button