Labarai

Malam Murtala Assada Sokoto ya caccaki baiwa badaru, Matawalle ministocin taro

Advertisment

Idan baku manta ba wannan can sati ne anka fitar da suwayen ko wane minista da ma’aikata da zaiyi aiki kwatsam sai anka ga dan kasuwa da malamin makaranta sikandare a matsayin babban minista da karamin minista Badaru Abubakar tsohon gwamnan jigawa babban ministan tsaro tsohon gwamnan zamfara karamin ministan tsaro wanda duk sun fito daga yankin arewa maso yamma, jiya litanin da an rantsar da su kowa ya shiga ofis domin fara aiki.

Malam Murtala Assada Sokoto ya caccaki baiwa badaru, Matawalle ministocin taro
Malam Murtala Assada Sokoto ya caccaki baiwa badaru, Matawalle ministocin taro Hoto/YouTube/ karatutunkan malam

Zakuji irin yadda malam murtala assada yayi gwamnatin tarraya wankin babban bargo a tsakiyar kasuwa akan sha’anin tsaro a arewacin najeriya inda malam yake cewa.

Tsakani da Allah babu abinda ya rage mana sai mu tashi muyita adu’o’i daman kun sabayi Allah duk mai nufin kasar nan da wata musifa , Allah ya mayar da musifar nan gareshi in yana shiryuwa Allah ka shirye shi yana daga cikin nade naden da ankayi a Nigeria kujera mafi hadari itace ta tsaro tsakaninku da Allah ganganci da ita ba ganganci ne da rayuwa yan Nijeriya bane?.

“To ku kalla ku gani an baiwa wanda basu da alaka ta kusa ko ta nisa da sha’anin tsaro tsakaninku da Allah akwai isgili ko babu isgili, abinda ankayi mana kamar misalin ka dauki limanin masallacin gana ka kaishi asibiti kace yayiwa mutane operation sai ace limamin nan baida alaka da harka likitanci sai kace Allah yake komai shi ke kashewa shi ke rayawa adaiyi addu’a Allah shike bada nasara,wallahi Allah bai bashi nasara saboda ba’a yi riko bil asbab ba.

Advertisment

Malam ya kara da cewa ka dauko mutumin da baisa sha’anin tsaro ba dan kasuwa ne dan siyasa ne ka dauki kujerar tsaro ka bashi kace ayi musu addu’a sai ka kalla kaga wallahi isgilina kakawa Allah abinda ba daidai ba kace ayi addu’a, a’a ayi riko da sababi Sa’a nan ayi addu’a.

Malam ya kara bada misali kamar a cika jirgin sama ne da mutane za’a kaisu saudiya sai a tare dan keke napep kace kai zo ka tuka jirgin nan ka kaisu saudiya sai ace baida alaka da shi sai ace Allah ka kai lafiya ko kai ka kai kudai kuyi musu addu’a su sauka lafiya, Allah bai sauka da su lafiya ba saboda ba’a yi riko da sabababi ba.”

Ku kalli wannan bidiyo domin jin cikakken bayyanin daga bakin malam murtala assada Sokoto a cikin wannan faifan bidiyo yayiwa Dr.Dauda lawan dare gwamnan jihar Zamfara yasani cewa Wallahi karya yarda da cewa gwamnatin tarayya zata taimakasa duk karya ce ka dauki yan banga mutum dari uku uku a kowane kamar hukumar guda goma sha hudu da gareku hausawa da fulani da jami’an tsaro a shiga daji wajen kamu su Bello turji tunda an san inda suke an san gidansu.

https://youtu.be/sc0ZOuBS9bw?si=Z8F26zUJgIU9D2Dy

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button