Labarai

Da yogot ya siye zuciyata, Zainab Yusuf, wacce ta hadu da mijinta a Twitter

Advertisment

Zainab Yusuf da Rayyan Tilde a wata tattaunawa da shafin BBC Hausa yayi da su sun bayyana yadda aka yi su ka hadu a Twitter har abin ya kai ga aure.

Zainab asali ‘yar Kano ce yayin da Rayyan Tilde dan Jihar Bauchi ne. Rayyan ya shaida cewa ya fara yi mata magana amma bata amsa mishi ba. Shafin LH na wallafa

Daga bisani akwai wani abokinsa, Sadiq Kurfi wanda shi ma ya san ta yayi masa iso gareta bayan ya je Kano.

A bangarenta, ta ce bayan ya yi mata magana sakamakon yadda mutane ke tura mata sako yasa bata duba nashi ba balle ta amsa har sai bayan Sadiq ya mata magana.

Advertisment

A zuwansa na farko ya kai mata Yogot wanda hakan ya yi matukar burgeta kuma washegarin ranar ne ranar zagayowar haihuwarta inda ya kara kai mata wata kyautar.

Rayyan ya ce kasancewar karamar kyauta yayi mata amma ta shiga farin ciki kwarai, hakan ya ba shi kwarin guiwa inda ya ji ta shiga ransa.

Ita kuma a bangarenta, ta ce da yogot din da ya kawo mata ya siye zuciyarta don tana son yogot sosai.

Yayin da aka tambayeta idan bayan ya kawo mata kyautar zagoyowar ranar haihuwarta ne su ka fara soyayya, cewa Zainab tayi:

“Eh gaskiya tun farko ma da yazo din, yogot din da ya kawo min ya siye zuciyata. Kuma da yadda ya gabatar min da kansa.”

Ta bayyana cewa ta kula da wallafe-wallafensa na Twitter akan addini yake yi sannan ko gyara zai yi wa mutum cikin mutunci yake yi ba cin fuska ba.

Ga bidiyon tattaunawar tasu da BBC Hausa:

 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button