Labarai

HIsbah ta bude kofar tuba ga Yan TikTok, wasu yan tiktok sun soma tsokaci

Advertisment

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta bude kofa ga Yan TikTok din da take nema da sauran wadanda suke aikata abubuwan da ba su da ce ba don mika wuya tun kafin ta yi ram da su.

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Dr. Mujahid Aminuddeen ya shaida wa Freedom Radio cewa duk wanda ya tuba zai je Hisbah don cike fom din yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsa da Hisbah.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan Hisbar ta yi muhimmin kamen da ya girgiza Yan TikTok.

Rahotonnin da Freedom Radio ta samu sun tabbatar da cewa tuni wasu da Hisbar ta ke nema suka arce.

Wasu sun koma Kaduna, Abuja har ma da Jamhuriyyar Nijar.

Mataimakin kwamandan hisbah ya kara da cewa

Muna fatan kafin azumin nan ya shigo kowa ya aje makamansa, kowa ya dawo da kayansa gaban Annabi, wanda sunka kwashe muna so kowa ya dai-dai tsakanin sa da Allah , domin abinda muke so shine kasan cewa rayuwar nan ba anan duniya bace kawai domin kasamu abinda idan ka mutu ka shiga aljanna da zaka sadu da Annabi Muhammad (S.A.W)”- inji maitamakin kwamandan hisbah.

HIsbah ta bude kofar tuba ga Yan TikTok, wasu yan tiktok sun soma tsokaci
Ummi shakira

Wasu yan tiktok da hukumar hisbah da take nema ya hada da Ummi shakira tana mai cewa.

“Daman ni duk abinda nake na daina kuma zan kara kiyayewa zan kara yin taka tsantsan , amma gaskiya sharfadi maganar zuwa gaskiya bazan iya ba, ina gudun ina shiga a rufe kofa, na riga na shiga hannu ba maganar fita sai da hali yayi.

Abinda zai hanamin jikina ya gayamin sai wani ikon Allah – inji Ummi shakira.

HIsbah ta bude kofar tuba ga Yan TikTok, wasu yan tiktok sun soma tsokaci
Balkisu Isah

Itama balkisu isah billy itama tace tana da wani hamzari ba gudu ba, domin bidiyon da ake yadawa tsofaffi ne

“Ni duk abinda anka ga nayi ba mai kyau ba dan Allah a gayamin inajin daɗi saboda iyayen mu da yawa basa son abinda muke yi, su ma ba’a a son ran su ba, wannan daman da hisbah ta bamu nagode sosai, in sha Allah daman ni, na riga na tuba, na tubawa Allah kuma na tubawa yan gari su da nake sawa suna gani.

Duk bidiyo na da kaga ana daukowa ana dorawa tsoffi ne, suma mutane ya kamata a dau mataki akan su”- inji Balkisu Isah.

HIsbah ta bude kofar tuba ga Yan TikTok, wasu yan tiktok sun soma tsokaci
Ashir Idris

To a nan munzo ga limami kuma shugaban samarin tiktok ashir Idris wanda anka fi sani da mai wushirya.

To kaga wanann kame-kame to ba shine zai magance muna ba yakamata a zauna, tunda an zauna an kara zama amma ana bama mutum dama ta ukku wannan dai shine fata na, saboda kowa yaga darasin abun ko yana ta shakku akan abun amma dai Allah yasa mudace, amma naji dadi da wannan magana da hisbah tace a zauna” -inji mai wushirya .

Mutane cikin gida da waje suna ta zurfafawa shugaban hukumar Hisbah Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da sauran ma’aikatansa akan irin wannan yaki da sunka dauko na dakile masu yada fala a cikin jihar kano.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button