Labarai

Babbar Musiba Ta Kunno A Kano, Budaddiyar Wasika Ga Gwamna Ganduje

Bayan sallama da fatan alkhairi, maigirma gwamna hakika jahar Kano ta sami kanta cikin mummunan yanayi wanda idan gwamnati ba tayi gaggawar daukan mataki ba wannan lamari ba zai haifar da d’a mai Ido ba, kuma ina da yakini cewa maigirma gwamna ba shi da cikakkiyar masaniya game da wannan fitina.
An sami wani Mutum da ake kira Abduljabbar Kabara da ke da’awar malunta, da kunnena na ji Malamai da mutanen gari da dama wadanda suka ce wannan mutumi yana zagin Annabi S.A.W sahabbansa da matansa, na ji wani malami ma da ya ce shi wannan mutumi Abduljabbar yayi inkarin tambayar Kabari da tashi daga cikinsa, sannan yana karyata ingantattun hadisan Manzo S. bayan inkarin ingancin Alqur’ani da yayi.
Bisa wannan lamari yau jahar Kano ta rikice, duk inda ka shiga jama’a kokawa suke da wannan musiba ta cin mutuncin Annabi, matansa, sahabbansa da magabata nagari suna kuma sukan gwamnatinka bisa rashin daukan mataki. Hakika mun shaide ka da dattako, kawaici da hakuri, an cutar da kai da dama kayi hakuri ba ka dauki mataki ba, amma taba Annabi, sahabbansa da matansa hakkin Allah ne da ba ya bukatar hakuri ko kawar da kai, babu musibar da ta kai taba mutuncin Shugaba S. idan aka cigaba da tafiya a haka Allah ka iya fushi da mu ya kuma debe mana albarka.
Ya maigirma gwamna soyyarka da kishinka ga addini a bayyane take ko ‘yan adawarka sun san haka, wannan ya sa ake maka lakabi da Khadimul islam, jama’a daga sassan duniya sun yaba maka bisa kokari da ka yi ta yi wajen ganin an hukunta Yahaya Aminu Shariff wanda yayi ‘batanci ga Annabi S.A.W amma sai bangarensa suka daukaka kara.
Ba wai jama’ar Kano kadai ke jin ciwo da abubuwan da wancan mutumi ke yi na cin mutuncin Annabi, sahabbansa da matansa ba, jama’ar Arewacin Najeriya ne da sassan kasashe, kuma na sha ganin rubuce-rubuce wanda suke sukar gwamnatinka bisa rashin daukan matakin dakile wannan barna. Ya maigirma hakika lamarin nan ba karamin tawaya, nakasu da koma baya ya kawo wa gwamnatinka daga wajen jama’a ba, kuma idan gwamnatinka ba ta dauki mataki ba zai iya zubar maka da daraja da kima wacce Allah ya baka tsawon shekaru.
Kano gari ne na addinin musulunci, akwai hukumomin gwamnati na addini da dama, na sha ji yadda Hisbah ke gurfanar da masu aikata abin da ya saba da musulunci a kotu, ya maigirma kama Aminu Yahaya Shariff amma a kyale wancan mutumi tamkar tufka da warwara ne, abun takaici ne da damuwa ace akwai gwamnati a sami wani yana taba martabar Annabi, sahabbansa da matansa amma gwamnati ta kawar da kai. Kowa na da damar yin addinin da ya so a dokar kasa, amma babu inda doka ta ce ka zagi addinin wasu ko ababen koyin addininsu wanda shi wancan mutumi Abduljabbar Kabara ke aikatawa.
An sami Malamai daga bangarorin Qadiriyya, Tijjaniyya da Izala wadanda ke Allah wadai da abin da wancan mutumi ke yi, sun nemi da ya zo su yi muqabala amma ya ki amsa tayinsu, watakila maigirma gwamna bai da masaniya, amma dama maigirma zai tattauna da malaman dake kusa da shi kan wannan lamari, za su tabbatar masa cewa gaskiya ne.
Bisa rashin daukan matakin gwamnati har takai an sami masoya manzo S.A.W sun fara tunzura suna kokarin daukar matakin dakatar da abun, wanda ko shekaranjiya na ga shi mutumin da ake kira Abduljabbar a wani bidiyo yana ingiza yaransa cewa duk wanda ya taba su su kwantar da shi su yanka shi, wannan furuci babban kalubale ne ga gwamnatinka da ma zaman lafiyar jahar Kano.
Ya maigirma tuntuni wannan mutumi ke zarginka cewa kana kokarin kashe shi, da kunnena na ji ya ce idan ka aiko aka kashe shi ba shi ka kashe ba wai Manzon Allah S.A.W ka kashe (Wal’iyyazubillah) wannan daya ne daga irin batancin da yake yi wa Manzo S. wannan mutumi ya yake ka matuka kuma yayi kokarin kayar da kai a zabe, na ji muryarsa wacce ya sha alwashin sai ya kaskantar da kai ya maigirma, haka nan ya ingiza mabiyansa suna zaginka tare da ci maka mutunci kawai don ka ki goyon bayan rashin gaskiya.
Na ga kalaman almajiran wannan mutumi da ke mayar da martanin cewa gwamnatinka ba ta isa ta dauki matakin doka a kan jagoransu ba. Ya maigirma Kano taka ce, kuma babu wanda ya fi karfin gwamnatinka, muna rokon maigirma da ya dauki matakin gaggawa bisa wannan mutumi domin Ice tun yana danye ake tankwara shi kuma idan an san farkon fitina ba a san karshenta ba, idan aka bar wannan lamari a haka ba a san abin da zai haifar na tashin hankali da tarzoma ba, rashin daukan mataki daga gwamnatinka zai tabbatar da ikrarin da wadancan mutane ke yi na fin karfin gwamnatinka.
Don Allah duk me kishin Annabi, sahabbansa da matansa wanda ke da ikon sada wannan sako ga maigirma gwamna ya taimaka ya sadar da shi.
Allah ya kiyaye al’ummar musulmi daga sharrin su Abduljabbar Kabara.
Daga Indabawa Aliyu Imam

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button