BIDIYO: Rike carbi ba bidi’a bane na gano hujjoji – Prof Shiekh Pantami


Fitaccen Malamin addinin musulunci dake Gombe a Najeriya, Shiekh Ali Isah Pantami ya ce bayan dogon bincike da nazari ya gano cewa rike carbi ba bidi’a bane don haka ya janye fatawoyin da yayi a baya tunda yanzu ya gano gaskiya
Shehin Malamin ya ce amma dai yana nan akan fatawar cewa yin tasbihi da hannu ya fi falala amma dai ya gamsu cewa mutum na iya amfani da carbi idan ya fi masa sauki.
“Da ina da fahimtar rike carbi bidi’a ne amma yanzu banda fahimta zanyiwa kaina tufka da warwara ko a addini bamu da fargaba da munyi zafi akan riƙe carbi amma yanzu bana yi saboda naga hujjoji kai tsaye rike carbi ba bidi’a bane amma fa ina rike da yi da yatsa yafi falala saboda wannan banida kokwanto wani zace wanda ya koyi yi carbi zai bata yatsa , ka bashi naira dubu dari nan take zai ƙirga bai ɓata ba ae bamuyiwa kanmu adalci ba wajen kirga kudi bazai ɓata amma da an kira Allah a nan zai ɓata.
Duk wanda yace idan za’a yi da yatsa za’a ɓata bashi kudi tsofaffi yan hamsin hamsin da yan dari dari da yan ɗari biyar da yan naira dubu daya nan kace idan ya kirgesu nashi ne kaga yadda ake buga lissafi , na ƙirga yan hamsin guda goma sha biyar 15 ya zama nawa dari 750 shikadai zai ƙirga su yan dari ya samu 21 ya zama nawa dubu biyu da dari daya.
Da yatsa nakeyi domin ina ganin yafi falala , da da muna zafi idan munga carbi kwacewa muke mu tsinka shi.
Gaskiyar magana na taba zuwa saudi Arabia shekarar 2005 haka niyi ta zagawa duk wanda nagani da taba zai karba in karya in yada haka nake da kazo gidan ka’aba kana shan taba larabawan nan sun sani ina karba nace ittaƙillah to da yamma tayi na fito duk inda anka san ina zama zaka ga ana gudu masu taba, inaga carbinka in maka nasiha.”
Ga bidiyon nan da malam ke fadi da bakinsa a lokacin da yake wajen majalishin sa.