Labarai

Zamu Fitar Da Yan Najeriya Miliyan 133 Daga Kangin Talauci A Nigeria – cewar Dr.Betta Edu sabuwa minista agaji da jin ƙai

Advertisment

Sabuwar Ministar Harƙoƙin jin kai da Yaƙi da fatara, Dr Betta Edu ta bayyana kudirin Gwamnatin Tarayya na fitar da ‘yan Najeriya Miliyan 133 Daga kangin talauci.

Beta Edu ta bayyana hakan ne a lokacin da ta fara aiki A Yau Litinin a Abuja tare da Gudanar da taron Gaggawa da manyan jami’an Hukumomin dake ƙarƙashin ma’aikatar.

Ta kuma Tabbatar wa ‘yan Najeriya Aniyar ta na tabbatar da Gaskiya da rikon Amana a lokacin da take rike da muƙamin Ministar.

Zamu Fitar Da Yan Najeriya Miliyan 133 Daga Kangin Talauci A Nigeria - cewar Dr.Betta Edu sabuwa minista agaji da jin ƙai
Zamu Fitar Da Yan Najeriya Miliyan 133 Daga Kangin Talauci A Nigeria – cewar Dr.Betta Edu sabuwa minista agaji da jin ƙai Hoto: Dr betta Edu/Instagram

“Abin da yafi muhimmanci shine, Zamu ci gaba da mai da hankali wajen fitar da ‘yan Nijeriya Miliyan 133 Daga Kangin talauci.

“Za kuma mu cimma wannan nasara tare da Goyon bayan siyasa mai ƙarfi Daga Mai Girma Shugaban ƙasa, Bola Tinubu da kowane memba na Majalisar Ministoci.

“Zamuyi wasa da Siyasa, mun zo nan ne don fuskantar hakikanin Harƙoƙin Mulki,” in ji ta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button