Labarai

Sun Ginawa Shugaba Buhari Ramin Mugunta Sun Fada Ciki ~ Datti Assalafy

Na tabbata inda miyagun ‘yan siyasa da suka tsara kwangilar zanga-zangar ENDSARS don su kawar da gwamnatin Buhari sun san zai yi sanadin daga martaba da darajar shugaba Muhammadu Buhari tare da dawowar tsoffin masoyansa da suka sauka daga mota wallahi da ba su fara ba
Miyagun ‘yan siyasa azzalumai ‘yan jari hujja wadanda suka saba neman shugabanci ta hanyar zubar da jinin talakawa da murdiyan zabe, ba shakka sunji kunya
Jama’a wannan ya zama darasi a garemu, shugaba Buhari babu abinda yake bamu muke sonshi, gaskiyarsa da adalcinsa shine dalilin da ya sa Allah Ya sanya soyayyarshi a zukatan mutanen kirki, kuma Allah Yake bashi taimako da nasara akan taron dangin miyagu mutanen banza
Don haka duk runtsi duk wuya muyi kokari wajen yin gaskiya da adalci ko da zuciyarmu bai so ba a rayuwa
A ‘yan kwanakin nan da aka fara zanga-zangar ENDSARS wanda ya rikide ya koma tarzoma da ta’addanci, na ga tsoffin masoya shugaba Buhari sun dawo sonshi a yanzu saboda sun fahimci gaskiya, hakika wannan babban nasarace
Yaa Allah Ka bawa shugaba Buhari ikon gyara kuskurensa, Allah Ka cika masa burinsa na alheri, Allah Ka bashi taimako da kariya akan miyagu makiya zaman lafiya
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button