Labarai

Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano Biliyan 30 kan rushe gine-ginen Masallacin Idi

Advertisment

A yanzu nan Majiyarmu ta samu wani labari wata kotu da ke birnin tarayya abuja taci tarar gwamnan jihar kano Engr. Abba kabir Yusuf (gida gida) tara akan rushe rushe da yayi kamar yadda Freedom Radio kano sunka ruwaito.

Babbar kotun Tarayya da ke zaman ta a Gyaɗi-gyaɗi a Kano ta umarci Gwamnatin jihar ta biya ƴan Kassuwar da ke da shaguna a filin Masallacin Idi da ke Ƙofar Mata Naira Biliyan 30 bisa rushe musu shaguna ba bisa ƙa’id ba.

Yayin zartar da hukuncin Mai Shari’a Simon Ameboda ya ce bin dare tare da rushe shagunan talakawa haramtaccen aiki ne mai cike da tsantsar zalunci da ƙeta, don haka lallai Gwamnati ta biya masu shagunan.

Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano Biliyan 30 kan rushe gine-ginen Masallacin Idi
Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano Biliyan 30 kan rushe gine-ginen Masallacin Idi

Haka kuma kotun ta hana Gwamnatin Kano shiga cikin filayen da yin tasirifi da shagunan balle bayar da su ga wani.

Advertisment

A wani Labari na daban : hukuma kwallon kafa taci James tara.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar England taci tarar kyaftin ɗin Chelsea Reece James.

Wannan na zuwa ne bayan da aka samu ɗan wasan da cin zarafin alkalin wasa a wasan da Chelsea tayi rashin nasara a hannun Aston Villa a ranar Lahadi.

Sai dai kyaftin ɗin na Chelsea na da damar mayar da martani har zuwa ranar 29 ga watan Satumba.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button