Labarai

Dan kunar-bakin-wake ya kashe mutum 52 a wurin Maulidi a kasar Pakistan

Advertisment

Lamarin ya faru a ranar Juma’a da safe kuma jami’an lafiya sun ce sama da mutum 50 sun jikkata sakamakon harin.

Akalla mutum 52 ne suka rasu sannan sama da 50 suka jikkata sakamakon wani harin kunar bakin-wake da aka kai a taron Maulidi a lardin Balochistan na Pakistan, kamar yadda jami’an lafiya da ‘yan sanda suka tabbatar, jaridar TRTAFRIKA Hausa na ruwaito.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin wanda yake zuwa a daidai lokacin da ake samun karuwar hare-hare a yammacin kasar.

Dan kunar-bakin-wake ya kashe mutum 52 a wurin Maulidi a kasar Pakistan
Dan kunar-bakin-wake ya kashe mutum 52 a wurin Maulidi a kasar Pakistan

“Dan kunar-bakin-waken ya tayar da bam din ne kusa da motar mataimakin sufuritanda na ‘yan sanda,” kamar yadda Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda Munir Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ya kara da cewa an samu tashin bam din ne kusa da wani masallaci wanda mutane ke taruwa domin bikin Maulidi, wadda rana ce ta hutu.

Kungiyar Tehrik-e Taliban Pakistan mai ikirarin jihadi ta musanta kai wannan hari.

Ana yi wa wadanda suka jikkata magani a wani asibiti da ke garin Mastung wanda ke kusa da inda lamarin ya faru.

A watan Yuli, sama da mutum 40 ne suka rasu a harin kunar-bakin-wake a arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa a yayin wani taron addini.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button