Labarai

BABBAR NASARA: ‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Ta’adda A Katsina (Hotuna)

Advertisment

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A kokarinta na dakile ayyukan yan ta’adda a jihar Katsina, rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin kwamishinan yan sanda na jihar, Alhaji Sanusi Buba, ta kama masu laifukkan ta’addanci, wanda suka hada da yan bindiga da masu satar mutane da fashi da makami da kuma masu satar dabbobi a jihar Katsina.

Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Katsina, ya bayyana hakan ne, lokacin da yake baje kolin masu laifin a helkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina a yau litinin.

Sanusi Buba ya kara da cewa mun kama su a garuruwan daban-daban na Jihar Katsina, kuma an samu bindigogi kirar AK47 da karamar bindiga guda biyar a hannun su da Kuma  Kama su day bindigogi kirar gida guda ashirin da biyar da motoci biyar da kuma Mashina hawa ashirin. Kuma ana cigaba da bincike.

Advertisment

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button