Labarai

Babu abinda zaka tsinanawa APC da Bola Ahmed Tinubu a 2027 kwankwaso ya caccaki Ganduje

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya caccaki abokin hamayyarsa na siyasa, Abdullahi Umar Ganduje, yana mai cewa babu wata uwa da zai tsinanawa jam’iyyar APC da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027.

A sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar NNPP Hon. Yakubu Shendam ya sanyawa hannu, ya mayar da martani ne kan kalaman da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Ganduje ya yi, inda ya ce Kwankwaso ba zai taɓa zama shugaban ƙasa a Najeriya ba.

Jam’iyyar ta ce idan aka yi la’akari da badaƙalar da ake zargin Ganduje da yi, bai kamata duk wani mai kishin Najeriya ya ɗauke shi da muhimmanci ba, inda ta ce badaƙalar ta yi wa tsohon gwamnan jihar Kanon lalatar da ba za a iya gyarawa ba, kuma ba zai iya kai Tinubu da APC zuwa matakin nasara ba a 2027.

“Ko a yarda ko aƙi yarda Ganduje ba shi da amfani ga Tinubu, haka jam’iyyarsa ta APC, da ƙasa baki ɗaya, zan iya rantsewa indai Ganduje ne shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, to Tinubu zai faɗi a zaɓen 2027 domin saboda shi kaɗai ‘yan Najeriya ba za su zabi Tinubu ba,” in ji Shendam

Ya kara da cewa, “Tinubu zai yi nadamar barin ‘yan Najeriya su riƙa ganin shi da Ganduje saboda shi ɗin mayaudari.

“Bari in tunatar da Ganduje cewa bayan ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamna, Sanata Kwankwaso ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa a shekarar 2003, sannan ya bashi S.A lokacin da ya zama ministan tsaro, ya da aka bashi muƙamin ES Chad Basin Development Commission, kuma daga bisa ya sake ɗaukar ka a matsayin mataimakinsa.

Sanarwar ta kuma nuna cewa Ganduje bai taɓa cin zaɓe ba a tsawon rayuwarsa sai wanda Kwankwaso ya tsayar da shi kuma ya ciyo masa zaɓen gwamnan kano a 2015.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button