Labarai

Zalinci Da Rashin Imanin Shugabannin Kasata Nijeriya

1. Lokacin da mutane sama da Miliyan Hamsin (50,000,000) ke gaza cin abinci sau biyu a wuni…

2. Lokacin da yara sama da Miliyan Uku (3,000,000) ba sa iya zuwa makaranta saboda talauci…

3. Lokacin da ma’aikata ke neman a rika biyansu N30,000 mafi karancin albashi a wata…

4. Lokacin da talakawa marasa lafiya sama da mutum Dubu Ashirin da Biyar (25,000), ke mutuwa saboda rashin kudin sayen magani…

5. Lokacin da Wutar Lantarki ta gagari unguwannin Malam Talaka…

6. Lokacin da Ruwan Sha mai tsafta ya fi karfin Talakawa…

7. Lokacin da ake yawan samun Haduran da ke lankwame rayukan gomman mutane saboda mutuwar tituna…

8. Lokacin da Talakawa sama da Miliyan Dari (100,000,000) ke gararanba da kamfar rashin tartibin muhalli…

9. Lokacin da ayyukan yi suka gagari dan Talaka a muhimman wuraren gwamnati…

10. Lokacin da Malam Talaka ke mantawa da dinka sutura shi da ahalinsa…

Lokacin ‘Yan Majalisun Kasarmu su Dari Hudu da Sittin da Tara (469) kacal! Suka bukaci a saya musu motocin hawa na kimanin Naira Miliyan Dubu Biyar da Miliyan Hamsin (N5.05b) don kawai su rika hawa.

Hakika! Wannan babban abin bakin ciki ne da takaici da kuma nuna rashin kulawa daga jagororinmu.

A matsayina na dan kasa, mai kishinta da son cigabanta, ba na goyon bayan wannan yunkuri na ‘Yanmajalisa, kuma ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Majalisar Dattijai Senator Ahmed Ibrahim Lawan, da na Majalisar Dokoki Femi Gbajabiamila, da kar su kuskura su amince da wannan yunkuri.

Allah Ta’ala Ya taimaki Talakan Nigeria!
Allah Ta’ala Ya taimaki Nigeria!

Muhammad Lawal Barista
8 Muharram, 1441 A. H.
8th September, 2019 C. E.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button