Toturials

Idan aka Goge (DELETE) Abu Akan waya ko Computer ina yake zuwa ?

Wannan dai tambaya ce mai mahimmanci da diyawa daga cikin mutane zasu bukaci sanin amsarta kasancewar abune da yake kamar al mara. Gashi dai dukkan abinda aka goge akan waya ko computer ba’a ganinsa yabi iska yatafi a zahiri amma kuma sai a nemeshi cikin wayar ko computer arasa, wai shin yaya abin yake? Biyoni sannu a hankali INSHA ALLAHU cikin wannan rubutun zanyi bayaninsa dalla dalla domin mukaru da ilmi da fasahar da ke kunshe a cikin wannan abinda mukasani na yau da kullum wato “DELETE”.

Kafin mukaiga tafiya Goge abu wato “DELETE” yanada kyau mufara fahimtar tayaya asali Memory Card ko Hard Disk ko Flash da kuma dukkan wata na’urar ajiya ke aiki a wannan zamanin hakan shi zai bamu damar fahimtar delete da kanta cikin sauki.
Na’am, Dukkan wata na’urar ajiya walau Memory card ko Hard disk ko Flash tamkar Estate yake wato Quarters, idan da zamu lura dukkan wani Quarters ko Estate da muka sani yanada suna, haka dukkan wani gida da yake Estate ko Quarters yanada Lambar Adireshi wanda ake amfani dashi wajen fayyace ko wane misali a cikin Quarters zakasamu Line A, Line B, Line C da sauransu haka kuma kowane gida da yake wadannan layukan yanada lambar adireshi misali Line A House Number 5 ko Line B House number 3 ko Line C House Number 12 da sauransu. Tamkar yadda muka kawo misalin Estate ko Quarters haka cikin Memory yake, cikin Memory ko Hard Disk yana dauke da gidaje kowane gida dake cikin nada adireshi na musamman ake amfani dashi wajen yimar lakabi ko nuni dashi. Wannan adireshi dashi babbar manhajar Computer ko Waya ke amfani dashi wajen fayyace wane gida yake acike kuma wani gida babu komai aciki, wadannan gidaje cike suke da “Bits” ko “Bytes”. Idan akace “Bits” ana nufin “0 ko 1”, Bits guda hudu ana kiransa “Nibble” wato rabin “Bytes” kowane “Bytes” kuwa Bits guda takwas (8) ne ke samar dashi wato Nibble guda biyu kenan.

Idan akace “Bytes” ana nufin mafi kankantan nau’in bayani (Information) da Computer ko waya ke iya tafiyar dashi dan yasamo ma’anarsa (Processing).

GAJERIN NAU’UKAN
Bits (Ana nufin 0 ko 1)
Nibble (Bits guda hudu)
Bytes (Bits guda takwas)
KiloBytes (Bytes guda 1024 ko 1000)
MegaBytes (KiloBytes guda 1024 ko 1000)
GigaBytes (MegaBytes guda 1024 ko 1000)
TeraBytes (GigaBytes guda 1024 ko 1000)
PetaBytes (TeraBytes guda 1024 ko 1000)
da sauransu.

Dan haka kamar yadda mukayi bayani da farko ko wane gida yana dauke da Bits ko Bytes haka kowane gida yanada adireshi. Wadannan adireshin dashi Computer ko Waya ke amfani wajen gane wane gida empty kuma wane gida ba empty ba, Sannan wadannan adireshin suna a tare ne a waje daya wato a Master Table. Ko wane abu waka ko hoto ko bidiyo ko file tarin Bytes ne. Daga lokacin da aka turawa Computer computer ko waya wani abu misali Wakar Shata mai suna “En yara gumina nakeci” Computer ko waya baza tataba sanin an turamata waka ba, illa dai ita abinda tasani antura mata Bytes wato tarin 0 da 1. Tun daga lokacin da ake kan turawa Computer ko Waya wani abu, a wannan lokacin farkon abinda Computer ko Waya zatayi shine dubiyar wane gidane dake cikin gidajen da Memorynta ko Hard Disk dinta da ke dauke dasu babu komai, ko kuma wane Adireshin gida ne babu shi cikin Master table dinta. Da zaran tayi roll call, misali ta duba akwai gida mai lamba 1 da kuma mai lamba 2 cikin master table dinta amma babu gida mai lamba 3 to zata ajiye wannan Bytes din wakar ne acikin gida mai lamba 3n sannan sai tasaka cikin Master Table list dinta cewar shima gida mai lamba 3 yanzu akwai abu aciki. Yawan gida da babu komai aciki shine yawan space dinda muke gani yasaura a hard disk dinmu ko Memory. Shiyasa da zaran kayi kokarin tura abu matukar Computar ko Wayar taduba cewa duka adireshin gidaje da Hard disk dinta ko Memory ke dauke dasu akwai shi acikin Master List Table dinta zatacema “Babu wajen kara tura abu face sai ka goge”.

Da zaran aka danna “DELETE” kan abinda akeso a goge, Computer zatayi dubiya ne cewar shine menene adireshin gidan da wannan abin yake. Sai dai yanada kyau mu fahimta adireshin file ko video ko waka da muke gani mu ‘yan adam yasha banban da adireshin da Computer ke gani domin ita tana amfanine da Hexadecimal wajen adireshin. Misali Yanzu idan muka tura abu a waya, kila ta Xender wato a wayar android kenan misalib adireshinsa zai zama kamar haka “/storage/emulated/0/Xender/Audio/Sunan wakar” to anan Computer ko waya batasamma wannan adireshin ba ita dai tana amfani ne da adireshin gidan da wakar yake misalin adireshin “00FFX10”, Sai mudauki misali Anaso a goge Waka mai suna Shata dake gida mai lamba “00FFX10” da zaran an danna “DELETE”, A guje Computer ko waya zataje cikin Master List Table dinta ta goge adireshin ma’ana zata goge “00FFX10”, kenan tunda yanzu Babu Adireshi mai “00FFX10” cikin Master List Table, dan haka wannan gidan Computer ko Waya a yanzu zata rinka kallonta ne a matsayin babu a cikinta komai tunda yanzu adireshin ta baya cikin Master List. Wannan shine ke tabbatar mana da cewa dukkan abinda kagoge a cikin waya ko Computer ba iska suke biba haka ma basa tafiya ko ina suna nan cikin Memoryn da ko Hard Disk, domin bayanin sama ya tabbatar mana Bytes din wannan abin yana cikin Computern ko Waya adireshin sane dai kadai Computer ko Wayar baya iya gani tunda ta riga ta goge shi cikin Master List. Shiyasa misali za’aga in an goge abu mai nauyin 1GB Computer ko wayar zata nunawa mutun akwai space din 1GB dukda cewar a zahiri abinnan da aka goge yana cikin Computern ko Wayar.

TO MEYASA IDAN AKA SAKE TURA ABU YAKE SAMUN DAMAR SHIGA TUNDA ANCE ABINDA AKA GOGEN YANA NAN BAI TAFI KO INABA?

Abu ne mai sauki, abinda aka goge da abinda ake kokarin turawa dukkansu Bytes ne wato tarin 0 da 1, kasancewar Computer da Waya na amfani da adireshine wajen duba akwai abu babu a gidajen Memorynta ko Hard disk, da zaran antura sabon abu Computern ko Wayar zataje ne wadancen gidajen ta sauya Bytes din farkon da na yanzu misali Bytes din farko 0011 1100 0101 0110 ne, na yanzu kuma 1010 1101 0110 0100 ne, to kawai zata sauya idan lambobin tsohon da sabon suka samu banbanci ne shine sannan tasake yiwa gidan sabon register a Master List dinta shikenan.
Haka zata rinka yima ko wane irin Memory ko Hard Disk.

TO MEYASA AKE IYAYIN FILE RECOVERY?

Recovery yana faruwa ne idan har Bytes din abubuwan basu samu sauyi ba acikin Memory ko Hard disk din, misali anada Memory mai 1GB yacika sai aka mar Format, ana iya dawowa da dukkan abubuwan dake ciki matukar ba’a tura sabbin files ba, domin idan antura wasu abubuwa bayan anyi format din mai nauyin 1GB koda anyi recovery sabbin abubuwan zai kawo ba tsoffin ba domin tsoffin yariga ya sauyu da sabbin.

Ga wadanda ke son sanin Yadda ake RECOVERY, akwai manhajoji da ake amfani dasu wajen yi kawai Ayi Search google kamar haka “File recovery software”.
Sannan akwai wadanda na sani gasu kamar haka
EaseUs
Recuva
Stella Data Recovery
MiniTool Power Data
The Ultimate Data Recovery.
.
Mai tambaya zai iyayi
Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
Repost.
08/09/2020.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button