Toturials

Http Vs https : Cikkakken Bayanin Bambamcin da ke Tsakanin HTTP Da HTTPS

Kasacewar yanzu zamani na cike ciken abubuwa a yanar gizo kama daga tallafi daga gwamnati da sauransu muna diyawa suna fadawa tarkon ‘yan damfara batare da ankara. Wannan shi yajawo hankalina domin nayi bayani ta yadda mutane zasu kare kansu daga fadawa tarkon ‘yan damfara ko kuma ince karawa kanmu ilmi ta hanyar sanin banbanci dake akwai sakanin HTTP da kuma HTTPS. A duk lokacin da zamuyi browsing dan lalumo wani abu a yanar gizo yanada kyau murinka lura shin wannan shafin HTTP ko HTTPS ke amfani dashi.

HTTP DA HTTPS mukan iya cewa kusan abu dayane banbanci dake sakaninsu kawai shine HTTPS yana amfani TLS da SSL (SECURE SHELL LAYER) wajen kai sako da kuma karbowa. Wannan SSL din wata hanya ce ta baiwa sakon da yake kaiwa da kuma karbowa tsaro ta hanyar canzasu daga asalin yadda suke saboda kar a gane menene sakon ke dauke dashi. Muna iya cewa dukkan shafi dake amfani da HTTPS yafi tsaro samada shafi mai HTTP kadai mara S. Biyoni dan bayani dalla dalla

MENENE HTTP?
HTTP yana nufin HyperText Transfer Protocol. HTTP matakalane ko ince dan aike ne dake kai sako da karbowa a yayin da ake kokarin neman abu a yanar gizo wato browsing, a duk lokacin da akayi kokarin neman wani abu a yanar gizo ta hanyar amfani da Computer ko Waya walau CHROME akayi amfani dashi ko Opera ko FireFox da sauransu HTTP yana kokarin yin wani abu wato HTTP Request da Response (Ma’ana aika bukata da kuma karbo amsa). Daga lokacin da mutun yayi amfani da browser misali yana searching a Google ko kuma yana kokarin shiga facebook ta hanyar rubuta adireshin facebook HTTP zai dauki bukatar wannan mutun sannan yaje shi amurka yakaiwa na’urorin Google ko kuma facebook cewar ga wane wane a waje kaza yana bukatar a budemar abu kaza ko kuma yana bukatar ganin abu kaza ko kuma yana bukatar amsar abu kaza, wannan sakon da yakai shi ake kira HTTP Request amsar da wadancan naurorin Google din ko facebook suka bashi wanda zai kawo wa mai kokarin searching a Google ko neman shiga Facebook din shi ake kira HTTP Response. A yayin da HTTP yake kokarin kai komo sakanin mai neman abu da kuma na’urorin wannan abun babu wani sirri a sakon da yake kaiwa domin kuwa yadda aka bashi haka nan zaikai wannan sakon koda kuwa Password ne, ko Lambobin ATM da kuma dukkan wani irin abu. Shi dai HTTP Request browser ne ke shiryashi ba tare mai browsing din yagani ba sannan kuma yabaiwa HTTP din yakai inda yakamata ga kuma misalin yadda HTTP Requests yake:

GET /index.php HTTP/1.1
User-Agent: curl/7.63.0 libcurl/7.63.0 OpenSSL/1.1.l zlib/1.2.11
Host: www.facebook. com
Accept-Language: en

Wannan shine misalin ire iren sakon Request da manhajar da ake amfani dashi yayin browsing zai shirya sannan ya baiwa HTTP yashiga yanar gizo yanemo inda yakamata yakai sakon sannan yakai. Matsalar da ke tattare da wannan anan shine dukkan wani mai ilmin HTTP ko Networking musamman ma hackers da zaran sunga wannan sakon sun san me yake nufi harma su karanta sannan su fahimta, a takaice yanzu haka acikin wadanda zasu karan rubutunnan akwai wanda sun riga sunma karanta kuma sun fahimta wannan shine babbar matsalar da ke tattare da shafi mai HTTP kadai batare da S ba, ma’ana babu tsaro ko kadan yayin da HTTP ke kai sako da kuma karbowa. Sakunan da HTTP ke baiwa kashi kashi ne misalin da muka bayar asama GET Request ne akwai irinsu POST Request wannan na faruwa ne yayin da mutun yayi submitting form sannan akwai irinsu REQUEST amma wadannan biyun sune wadanda akafi aiki dasu wato GET da POST.

A yayin da HTTP yakai sako sannan na’urar da aka kaimar sakon ya karba misali na’urar Facebook ne aka kaiwa sakon, ga misalin amsar da shi kuma zai mayar

HTTP/1.1 200 OK
Date: Fri, Oct 2020 12:14:39 GMT
Server: Apache
Last-Modified: Thur, 22 Oct 2020 11:1
Accept-Ranges: bytes
Content-Length: 12
Vary: Accept-Ecoding
Content-Type: html

Sai kuma dukkan abinda yakamata agani a shafin farko na facebook din mutun anan.

Indai ba shafi mai amfani da HTTPS bane to wannan amsar da na’urar facebook yabaiwa HTTP yadda muka ganshi a saman nan haka zai daukoshi tun daga amerikan yakawowa wanda ya bukata. Na tabbata koda mutun baida ilmin Computer amma yana iya karanta turancin da ke cikin sakon. Suu kuwa hackers dama cen da ilminsu na Computern dan haka suna ganin hakan zance yakare domin sun riga sunsan abinda hakan ke nufi.

MENENE HTTPS?
HTTPS yana nufin HyperText Transfer Protocol Secure wannan S din shaida ne dake nuna cewar sakon da HTTP zai kai sannan yakarbo amsar tasamu wani tsaro, wannan sakon zai tafi ne a matsayin “Encrypted”. Maimakon ace Hackern yaga sakon kamar haka:

GET /index.php HTTP/1.1
User-Agent: curl/7.63.0 libcurl/7.63.0 OpenSSL/1.1.l zlib/1.2.11
Host: www.facebook. com
Accept-Language: en

Wannan S din zai canzawa sakon halitta daga asalin sa ya maidashi wani abu kamar:

t8Fw6T8UV81pQfyhDkhebbz7+oiwldr1jgHBB3L3RFTRsQCpaSnSBZ78Vme+==

Na tabbata daga ganin wannan rubutun zaiyi wuyan karantuwa dan haka koda Hackern yagano yaya asalin abinda yake zai dan sha wahala.
Dan haka yanada kyau murinka lura da shafukan da muke ziyarta musamman shafukan da za’a buka cemu mubada Sensitive Information irinsu bayanai gameda asusun bankinmu, password din mu da sauransu. Sannan wannan bashi ne kadai hanyoyin kaucewa tarkon hackers ba illa dai yana cikin matakan kariya na farko farko yanada kyau mu fahimta a ka’idar Hackers babu wani abu wai Security domin cewa ma suke “Security is an illution” wato wani abu ne kamar mafarki ko kuma wani abu kamar kawalwainiyya dake saman teku ko kan kwalta dan haka ana hadawa da wasu hanyoyin tsaron yafi.

YAYA AKE GANE SHAFI MAI HTTPS?
A duk lokacin da a ziyarci shafi a lura da kyau da duba inda aka rubuta adireshin, indai akwai alamar makwalli to HTTPS ne akasin hakan kuma HTTP ne.

Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
07068345068
23/10/2020.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button