Toturials

Yadda Zaka Maida Wayarka 4G Network Koda Wayar Taka 3G Network Ce Ta Hanyar Amfani Da Forcelte.

Jama,a Assalamu Alaikum Warahamatullahi Barakatuhu, Barkanmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka

A Cikin Posting Din Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Ne Akan Hanyar Da Zakabi Ka Karawa Wayarka Saurin Browsing.

Abin Tambaya Wannan Wace Hanya Ce ? Amsa Wannan Wata Sabuwar Hanya Ce Da Zakabi Domin Ganin Ka Cimma Nasara Ka Kawar Da Matsalar Da Take Damunka Na Slow Browsing.

Tayaya Zanyi Wannan Aiki Na Mayar Da Wayata Daga 3G Network Ko 2G Network Zuwa 4G Network ? Wannan Abu Ne Mai Sauki, Abinda Zakayi Kawai Shine Kaci Gaba Da Karanta Wannan Bayani Namu Domin Sanin Yadda Zakayi Wannan Aiki.

To Da Farko Dai Minene Ma, Network 2G Ko 3G? Amsa Shi Network 2G Ko 3G Wata Manhaja Ce Ko Wani Abune Da Aka Kirkireshi Wanda Yake Idan Babu Shi To Kwata Kwatama Waya Bazatayi Browsing Ba.

To Kaga Kuwa Dole Sai Dashine Mutum Zai Iya Yin Browsing Da Wayarsa.

To Minene Matsayin 2G Da 3G ? Amsa Shi Network 2G Shi Aka Fara Futarwa A Tsarika Irin Na Network, Amma Daga Baya Sai Aka Fitar Da 3G, To Shi Network 3G Yafi 2G Sauri Da Gaggawa.

Domin Kuwa Idan Zaka Dauko Abu Ko Film Mai 100Mb To Zaka Dauko Shine A Tsakanin Minti Ashirin Zuwa Goma, Yayin Da Idan Da 2G Kake Amfani Zaka Iya Kaiwa 30 Minute Ko 40 Minute Kaga Kuwa Lalle Wannan Banbanci Ne Mai Tsawo.

Shi Kuma 4G Network Shine Wanda A Yanzu A Nigeria Ake Amfani Dashi Shi Wannan Network Yafi Kowanne Karfi, Domin Kuwa Gudunsa Yakai Idan Zaka Dauko Abu Mai Nauyin 100Mb To Idan Da 4G Network Ne To Zaka Dauko Shi A Minti Biyar Zuwa Goma.

Kaga Kuwa Wannan Tazarace Mai Yawa Da 4G Network Yayiwa 3G Da 2G Network, A Yanzu Dai An Kirkiri 5G Network Amma Har Izuwa Wannan Lokaci Da Nake Bayani Bai Samu Isowa Nigeria Ba.

To A Cikin Wannan Application Mai Suna Forcelte, Zamu Kawo Muku Bayani Akan Yadda Zakuyi Amfani Dashi A Wayoyin Da Version Dinsu Yakai Daga Biyu Zuwa Goma Sha Daya.

To A Karshen Wannan Bayani Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Application Sannan Zaku Iya Saukar Dashi Daga Manhajar Playstore Domin More Wannan Garabasa.

Sannan Bugu Da Kari Idan Wayarka Ma 4G Ce To Zaka Iya Amfani Da Wannan Application Domin Karawa Wayar Taka Saurin Browsing Akan Wanda Takeyi.

To Da Farko Bayan Kadauko Wannan Application Zakagayi Installing Nasa Daga Nan Sai Kayi Open Zaka Danna “Next” Sau Daya Daga Nan Zakaga Wani Wuri An Rubuta ” Permission” To Saika Danna Wannan Wuri Ka Bashi Wannan Dama Daya Bukata Daga Nan Saika Kara Danna Next.

To A Shafi Na Gaba Zai Kara Neman Ka Dan Taba Wani Dan Box Wato Akwati A Sama Kadan Shima Dai Dama Yake Bukata Kabashi Wanda Zai Hau Kan Wayarka To Bayan Ka Taba Wannan Dan Akwatin Sai Ka Kara Danna Get Started.

Daga Nan Zai Kawoka Wani Shafi Da Zai Baka Zabi Ko Ince Rubutu Layi Biyar, To Kai A Rubutu Na Daya Zuwa Na Biyu Zabinka Yake.

A Zabi Na Farko Dai Idan Wayarka Version Dinta Baikai 11 Ba To Zaka Danna Wannan Na Farkon, Domin Kuwa Shine Dai Dai Da Wayarka Idanma Ka Danna Na Kasa Kazaiyiba Tunda Wayarka Batakai Version 11 Zuwa Sama Da Hakaba.

Idan Kuma Wayarka Takai Version 11 Zuwa Sama Da Haka To Saika Danna Na Biyu Wanda Shine Dai Dai Da Wayarka.

To Koma Dai Wanne Ka Danna Abinda Zakayi Iri Dayane Da Abinda Wancan Zaiyi, Abinda Zakayi Shine Idan Ka Dan Kalli Kasan Rubutun Zakaga Wasu Rubutu Da Yawa To Babu Ruwanka Dasu Abinda Zaka Duba Shine Wurin Da Aka Rubuta ” GSM/WCDMA/LTE ( PRL ).

To Saika Danna Kan Wannan Rubutu Daga Nan Zakaga An Watsoma Network Kala Kala Daban Daban To Saika Duba ” LTE ONLY “Saika Danna Shikenan Daga Nan Wayarka Zata Kara Sauri Na Browsing Koda Bata Sauri A Baya.

Mungode Mungode Mungode Yanzu Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Application Domin Ku Samu Saukin Saukar Dashi Izuwa Kan Wayoyinku Zaku Danna Kan Ko Wurin Da Aka Rubuta ” Download FORCELTE Now ” Domin Downloading Na Wannan Application.

Via Hikimatv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button