Toturials

Abinda Baka Saniba Dangane Da Saurin Karewar Da Kudin Wayarka Keyi ( Airtime ) A Dan Kankanin Lokaci.

ama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Wannan Lokaci Sannunmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Tasha Tamu Mai Albarka

Inda A Cikin Darasin Da Zamu Koya Muku Ayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakayi Maganin Matsalar Yawan Debe Maka Mudade Ko Yawan Zukar Maka Katin Wayarka A Lokacin Da Kake Kira.

Wannan Matsala Dai Na Daya Daga Cikin Matsalolin Dake Ciwa Mutane Tuwo A Kwarya Shekara Da Shekaru.

Wannan Na Faruwa Ne Saboda Rashin Sanin Mike Faruwa A Duniyar Yanar Gizo Gizo Da Mutane Sukayi.

Kamar Yadda Mukayi Alkawarin Kawo Muku Bayani Akan Yadda Zakuyi Maganin Wannan Hanya,To Yanzu Zamu Muku Bayani Dalla-dalla.

Da Farko Idan Ana Yawan Ja Ko Cinyema Kudi Cikin Kankanin Lokaci A Lokacin Da Kasa Kati A Wayarka To Yana Da Kyau Kasan Wannan Itace Matsalarka.

Akwai Plan Ko Ince Tariffic Plan Daya Kamata Kasani Wanda Anan Ne Zaka Zabi Tsarin Da Baza,ana Yawan Jamaka Kudade Sosai Ba.

To Plan Din Dayafi Ko Wanne Dadin Harka Shine “Bizplus” Bayan Wannan Plan Din Sai “Pulse” Saikuma “Mpulse”
To Wadannan Tsarika Guda Uku Sunfi Sauki Wajen Kira.

Dalili Shine Su Wadannan Tsarika Basa Bada Bunus Musamman Ma Bizplus, Amma Mpulse Suna Dan Bada Bunus Kuma Yana Da Dadin Kira Da Sauki.

Haka Shima Pulse Basa Bada Bunus Na Kira Sai Dai Bunus Na 10Mb A Duk Lokacin Da Kasa Katin Naira Dari Zuwa Dari Biyu.

Wannan Kenan Dangane Da Yadda Zaka Shiga Tsari na Kira Mai Sauki Ba Wanda Za,ana Janyema Kudaden Kaba.

Matsala Ta Biyu Itace Yadda Kake Ko Wani Yake Saka A Wani Tsari Daban Wanda Anan Suke Kwashe Maka Kudi Idan Kayi Recharge.

Wannan Matsalar Itama Tana Faruwa Ne Batare Da Mutum Ya Ankareba, Domin Kuwa Wasu Lokutan Kamfanin MTN Suna Turowa Mutum Notification Na Sako Wanda Maimakon Kayi Cancel Sai Ka Danna Ok.

To Kasani Kana Danna Ok Ka Shiga Wannan Tsari Kuma Zasu Rika Daukan Naira Hamsin Hamsin Ko Dari Dari Koma Sama Da Haka.

To Da Zarar Kaga Irin Wannan Notification Din Sai Kayi Hanzarin Danna Cancel, Idan Kuma Ka Riga Ka Danna Ok To Ga Hanyar Dazakabi Domin Fita Daga Wannan Tsari Da Kake Ciki.

Sannan Akwai Masu Sayen Data Su Danna Wurin Da Aka Rubuta Auto Renewal, To Ba,a Danna Wannan Wuri “One Off Purchase” Ake Dannawa Wato Sau Daya Kake Son Saya Bawai A Dunga Sayamaba.

Numbobin Dazaka Danna Koda Baka Sani Ba Cewar Kataba Shiga Wani Tsari Ko Kuma Kanaso Ka Tabbatar Dacewar Baka Cikin Wani Tsari To Saika Danna *447# Daga Nan Saika Danna Wurin Da Aka Rubuta “Active Service” To Anan Zakaga Tsarikan Da Kake Ciki Wanda Kasani Dama Wanda Baka Sani Ba.

Idan Kuma Hakan Bai Yiwuba To Zaka Iya Kiran Call Center Nasu Kamusu Bayanin Abinda Ke Faruwa Number Na Call Center Din Shine 180.

Mungode Mungode Mungode Kadda Ku Manta Da Makalewa Shafin Hikimatv Domin Samun Sababbin Darusa Dasuka Dangancin Wayoyin Android Dama Sauran Abubuwan Da Zamani Yazo Dasu.

 

© Hikimatv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button