Toturials

Yadda Zaka Dakatar Da Wayarka Ta Android Daga Kamewa Da Karewar Chaji Da Wuri.

A Cikin Darasin Namu Nayau Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakayi Maganin Matsalar Kamewar Waya A Lokacin Da Kake Amfani Da Ita.

Sannan Zamu Kawo Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zakayi Maganin Matsalar Karewar Chaji Cikin Kankanin Lokaci.

abinda muke bukata shine ka karanta wannan bayani tun daga farko har karshe domin fahimtar abin yadda yakamata.

To akwai dai hanyoyi guda biyu dazakabi domin magance wannan matsala hanya ta farko itace ta hanyar danna alamar ” Do Not Disturb “.

Sai dai ita wannan alama ta do not disturb bata fiye zuwa a kananan wayoyi ba, idan waya bata wuce version 9,10,11 Ba to wannan alama zaiyi wuya kasameta a kan wannan waya.

To idan wayarka tana da wannan alamar kai tsaye zaka danna wannan alama, wannan alama tana nan idan ka jawo saman wayarka kamar zaka bude datar wayarka ko zaka bude blutouth to anan idan kabi sunayen abubuwan dake wannan wuri to zakaga wannan alama ta do not disturb.

Saika dannata danna wannan alama zai dakatarma da duk wani application dayake shamaka chajin wayarka ko yake kamarma da waya batare da kasani ba.

Idan kuma wayarka kasa take da version 9 To Hanyar dazakabi itace, zaka shiga setting na wayarka, daga nan zakaga wurin da aka rubuta apps ko apps management ya dai danganta da yadda wayarka take.

To anan zaka danna wurin da aka rubuta apps ko app management anan zai kaika shafin da zakaga dukkan wani application da kayi installing dinsa, to anan saika danna irin facebook.

Bayan ka danna kan facebook zai watsoma wasu bayanai dangane dashi to anan zaka nemi wurin da aka rubuta notificatios, idan kaga wannan wuri saika danna to anan zakaga wata yar kibiya a bude saika rufeta.

Haka zakayiwa ko wane application da yake watsoma da tallarsa koda baka hau kansaba misali irinsu whatsapp, opera, Youtube, Vidmate Da Dai sauran application din da sakonninsu yake damunka.

To yin hakan zaiyi matukar tasiri wurin rage maka yawan kamewar da wayarka takeyi,sannan zai kara ragewa wayarka yawan shan chaji akan yadda takesha a baya.

Sannan yawan rage hasken screen na waya shima yana taimakawa wurin ragewa waya shan chaji, har ila yau amfani da application kadan shima yana taimakawa wurin yin amfani da wayarka cikin kwanciyar hankali.

Wannan kadan kenan daga cikin abubuwan da muka zakulo muku dangane da abubuwan dakesa wayoyinku sukasance masu yawan shan chaji dakuma kamewa.

Inda dukka dukka anan muka kawo muku karshen wannan darasi inda muke fatan zaku kasance da wannan shafi namu mai albarka Hikimatv domin samun sababbin shirye-shiryenmu akowane lokaci.

©Hikimatv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button