Toturials

Yadda Zaka Saukar Da Kowane Irin Video Daga Shafin Tiktok Batare Da Kaga Alamar Tiktok Watermark Ba.

Jama,a Assalamu Alaikum Barkanmu Da Sake Saduwa Daku A Cikin Wannan Shafi Namu Mai Albarka Hikimatv.

A Posting Din Dazamukawo Muku Yau Zamu Muku Cikakken Bayani Akan Yadda Zaka Saukar Da Duk Wani Video Da Kake Bukata Daga Shafin Tiktok, Koda Kuwa Mai Videon Ya Rufe Wurin Downloading.

A Nutse Saiku Biyomu Ku Kuma Saurari Ko Muce Ku Karanta Wannan Bayani Tun Daga Farko Har Karshe Domin Ku Fahimci Yadda Zakuyi Wannan Aiki Batare Da Kun Samu Wata Matsala Ba.

To Da Farko Dai Hanyoyin Downloading Na Video Daga Shafin Tiktok Guda Biyu Ne, Saboda Haka Yanzu Zamuyi Bayani Akansu Daya Bayan Daya.

( 1 ) Hanya Ta Farko Itace, Ta Hanyar Download Kai Tsaye Daga Cikin Manhajar Tiktok,wanda a cikin wannan application idan ka danna wata alama mai kamar kibiya daga hannun dama to zai watso maka options da hausa ana nufin zabi to anan zakaga wurin da aka rubuta save video ko download video saika danna wannan wuri take videon zata fara downloading.

Idan kuma bakaga Wannan Wuri Ba To Wannan Video An Rufe Mata Download A Hausance Mai Wannan Video Bayason Kowa Ya Mallaketa.

Saboda Haka Idan Har Hakan Ta Kasance To Kana Da Zabi Na Biyu Wanda Shine Kuma Na Karshe Kuma Shine Wanda Zai Dan Batama Lokaci.

Wannan Zabi Kuwa Shine, Zaka Saukar Da Duk Wani Video Ne Daga Shafin Istagram Ta Hanyar Amfani Da Copy Link.

Kai Tsaye Kamar Yadda Mukayi Muku Bayani A Baya Idan Ka Danna Kan Wannan Alamar Mai Kamar Kibiya,Bayan Ka Danna Wannan Alama Zai Kara Baka Wasu Option Din Wato Zabi Zakaga Irin Share, Copy Link, Ko Kuma Link, Yadai Danganta Da Yadda Wayarka Ta Baka.

To Idan Ka Danna Kan Copy Link Ko Link Saikayi Back Ka Bude Opera Mini Takan Wayarka Ko Google Chrome A Takaice Dai Yafi Kyau Kayi Amfani Da Google Chrome Ko Ince Chrome Kai Tsaye Idan Ka Shiga Cikin Wannan Application Mai Suna Chrome Kadda Fa Ka Damu Kowace Waya Indai Babbace Ba Karama Bace Tana Da Google Chrome.

Bayan Ka Shiga Chrome Saika Danna Wurin Da Ake Rubutu, Anan Saika Rubuta ” Musical Down” Ka Danna Search Daga Nan Zai Watsoma Site A Rubuce Zakaga An Rubuta “Musicaldown”Saika Danna Kan Wannan Rubutu Daga Nan Zai Kaika Zuwa Cikin Wannan Site.

To Anan Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Enter Your Tiktok Video Or Song Link, Sannan Daga Gaba Zakaga Wata Yar Alama A Gaban Rubutun To Saika Dannata Nan Take Zakaga Link Din Videon Dakayi Copy Ya Fito A Cikin Wannan Wuri,Saika Danna Alamar Download.

Daga Nan Zai Kaika Shafi Na Biyu Wanda Anan Ne Zakaga Wurin Da Aka Rubuta Download Mp4 Now Saika Danna Take Zai Fara Download Kai Tsaye, Idan Kuma Yanemi Permission To Saika Danna Alamar Allow Domin Ka Bashi Damar Fara Download.

To Wadannan Sune Hanyoyi Guda Biyu Wadanda Zakabi Domin Saukar Da Video Ko Waka Daga Kan Tiktok Batare Da Kaga Alamar Watermark Ba.

Yanzu Zamu Ajiye Muku Link Din Wannan Site Din Kai Tsaye Domin Kusamu Saukin Download Na Videos Daga Wannan Shafi Na Tiktok.

Ga Link Dinnan Saiku Danna Kansa Zakuga An Rubuta “Musicaldown “.

Mungode Mungode Mungode Saimun Hadu Daku A Cikin Wani Posting Din A Nan Gaba Sannan Kadda Ku Manta Da Danna Alamar Allow Na Notification Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu A Kowane Lokaci.

Source Hikimatv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button