A makon da ya gabata an karade dandulan sada zumunta a Nigeria da batun samun lasisi da kamfanin SpaceX ya yi, don fara gudanar da ayyukansa a Nigeria a kan wani tsarinsa mai suna Starlink. Don haka na kudiri niyyar yin bayani a kan wannan tsari da yadda zai kawo canji a kasarmu ta gado.
Starlink wani tauraron Dan-Adam ne da ake kira satellite, wanda ya kasance mallakin kamfanin SpaceX wanda shahararren attajirin duniya Elon Musk yake jagoranta. An samar da Starlink a shekarar 2015, wanda ya kasance satellite ne da aikinsa kawai shi ne bayar da “internet access” ga na’urori.
Wato dai kamar yadda ka san satellite din da ke gidanka, kake kallon wasanni ko labarai, to haka nan shi ma Starlink aikinsa shi ne ba ka “internet access” a gidanka a na’urarka kamar yadda MTN ko Airtel za su ba ka kai-tsaye ta ka yi amfani Wi-Fi.
Amfanin Starlink
A maimakon ka kafa dogon karfe (mast) a gidanka, ko masana’anta, ko asibiti, ko makaranta, ko wata unguwa daban wanda za ka rinka amfani da Wi-Fi da kamfanin MTN ko Airtel ka rinka biyansu duk shekara su kuma su rinka ba ka “internet access”, Starlink ya zo da tsarin da ba sai ka kafa dogon karfen nan ba, kawai “satellite dish” ya ishe ka.
Abun da kake bukata kawai shi ne “satellite dish” da sauran kayan hada shi wanda idan ka saya za a ba ka a cikin wata jaka da ake kira Starlink Kit.
A yanzu haka, matukar dai ba ka shahara a kudi ba, ba lallai ba ne na iya tunani kai-tsaye cewa kana da Wi-Fi a gidanka. Watakila sai dai a manyan makarantu, ko kamfanoni ko gidajen gwamnati.
Amma Starlink ya zo da tsarin da zai ba ka “internet access”a gidanka kamar yadda kake amfani da satellite a gidanka kake kallon wasanni ko labarai. Ba ka bukatar wasu makudan kudade don fara amfani da shi. Za ka iya jona na’urori sama da dari a lokaci guda.
Tasirin Starlink
Babban tasirin da Starlink ya samu shi ne yadda yake aiki cikin sauki da kuma sauri. Zai magance yadda ake samun matsalolin “network” da tsadar hawa yanar gizo na’urorinmu na gida. A cewar kamfanin, so yake ga magance matsalolin shiga yanar gizo ga karkara (kauyuka) da wuraren da suke shan wahalar samun damar shiga yanar gizo.
Yadda ake amfani da Starlink
Abu na farko da kake bukata don fara amfani da Starlink shi ne sayen shi. Da zaran ya zo Nigeria, za ka iya shiga shafinsu na yanar gizo starlink.com ka zabi wurin da kake (adireshinka), sannan ka cike fom ka duba tsare-tsarensu na biyan kudi da makamantansu.
Da zaran ka gama za su kawo maka wata jaka da ake kira Starlink Kit, a cikin jakar akwai duk kayayyakin da ake bukata wajen saitawa, kamar su router, cable, dish da sauransu da kuma bayani a kan yadda ake amfani da su.
Muhimman Bayanai
—Starlink ba tafi-da-gidanka ba ne, don haka ba za ka iya amfani da shi duk inda kake ba, sai dai a inda aka saita shi —kamar dai yadda kake amfani da satellite dinka a gida
—Mutane sama da 400,000 suna amfani da shi a fadin duniya
—A yanzu akwai tauraron Dan-Adam mallakin Starlink sama da 2,300 a sararin samaniya
—Yana da matukar saurin da za ka iya sauke abu a kan 100-200mbps
—Mohiddeen Ahmad
Scientist, technologist, Founder/CEO of Stackplaza