Addini

An ci zarafin Annabi ﷺ a zamanin baya, amma bai taɓa bayarda umarni a kashe kowa ba. ~Cewar Sheikh Ahmad Gumi

Fitaccen malamin addinin Islama, mai suna Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa a zamanin Annabi SAW ma, an ci zarafinsa amma bai taɓa kashewa ko bayarda umarni a kashe wani.

Gumi ya bayyana hakan ne jiya, yayin da yake wa’azi a babban masallacin Juma’a dake Jihar Kaduna.

Malamin, ya bayyana cikin wani bidiyo cewa, Annabi (SAW) ya kawar da kai duk da irin cin zarafin da waɗanda ba Musulmi ba, suka yi masa a wancan zamanin, saboda baya son a danganta shi da zalunci.

Ya bayyana haka ne, dai-dai loƙacin da yake sharhi dangane da kisan wata ɗaliba da wasu fusatattun matasa su ka yi, sakamakon zargin ɓatanci a Jihar Sokoto.

Ya ƙara da cewa, hanyar da mutum zai nuna yana son Annabi ita ce wajen koyi da irin halayensa.

Musulmai da Kiristocin Nigeria sun aminta su zauna cikin zaman lafiya, saboda haka duk waɗanda suke da hannu wajen kashe ɗan Adam, toh ba za su sansani ƙamshin Aljanna ba na tsawon shekaru 40.

Kamar yadda Jaridar PRNigeria ta ruwaito, Gumi ya ƙara da cewa babu wanda yake da hurumin ɗaukar doka a hannun kamar yadda Addini ya koya, tare da yin kira kan Maluman addini su rinƙa koyar da mabiyansa ainihin koyarwar addinin Islama ba tunzura su ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button