Addini

Abin da ya sa hisbah ke kai samame wuraren horewa a kano – Sheikh Aminu Daurawa

Hotuna da bidiyon, da ke nuna ‘yan Hisban na kama ‘yan mata da ma samari a wuraren holewar, sun karaɗe shafukan sada zumunta

Muhawara da cacar baki sun kaure a ciki da wajen Kano, kan abin da wasu ke cewa gagarumin kame ne kan masu yawon ta-zubar da jami’an Hizbah suka ƙaddamar.

Abin da ya sa hisbah ke kai samame wuraren horewa a kano - Sheikh Aminu Daurawa
Abin da ya sa hisbah ke kai samame wuraren horewa a kano – Sheikh Aminu Daurawa

Majiyarmu ta Bbchausa na ruwaito.Hotuna da bidiyo sun cika shafukan sada zumunta na ‘yan hizba cikin duhun maryace, suna daƙume ‘yan mata, da ma samari a wuraren yawon dare.

Ba sabon abu ba ne kamen mutane a wuraren da ake zargi ana aikata karuwanci ga hukumar Hizbah ta Kano, sai dai ga alama, wannan ya kama hanyar shiga jerin ayyukan hizbah da suka fi tayar da ƙura da janyo ka-ce-na-ce.

Wasu dai na kallon samamen a matsayin wani muhimmin aikin da aka kafa Hukumar domin aiwatar da shi, wato hana aikata baɗala, kamar yawon dare da masha’a da sheƙe aya, kai har ma da karuwanci a birnin Kano.

Wasu kuwa na ganin duk da yake, ‘yan hizbar ‘aikin Allah’ suke yi, amma zakewa da kokawa ko ruƙunƙumar ‘yan matan da ake ƙoƙarin kamawa da karya ƙofar gida ko ɗaki, abubuwa ne da suka wuce gona da iri.

Yayin da wasu ma ke fitowa gaba-gaɗi suna zargin Hizba da keta haƙƙin ɗan’adam.

Sai dai masu kare dirar mikiyar Hizbah na cewa kushe hukumar a kan wannan sabon yunƙuri, tamkar nuna goyon baya ne da kuma rufe ido ga iskance-iskance da lalacewar da ke ƙaruwa a kan tituna.

Ga kalaman Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa game da al’amarin da Bbchausa na zanta malamin.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button