Addini

Kungiyar IZALA tayi Allah wadai da zagin Annabi (SAW) da wata yarinya tayi a jihar Sokoto

Hukuma ce ke da hurumin yanke hukunci ga wanda ya zagi Annabi, ba ‘dai’daikun mutane ba

Kungiyar wa’azin musulunci ta Izalatil Bidi’ah wa iqamatis sunnah a tarayyar Naijeriya tayi Allah wadai da wata yarinya wacce ba musulma ba da ta zagi Annabi Muhammadu tsira da aminci su kara tabbata a gare shi . Yarinyar mai suna Debora wacce ke karatu a kwalejin Ilimi dake jihar sokoto, tayi mummunan zagi a wani zaure na WhatsApp da suka bude a matsayin su na dalibai domin tattaunawa, Yarinyar ta kunduma ashariya ga Annabi (SAW) wanda duk musulmi bazaiji dadi ba, wanda hakan har yakai ga wasu jama’a suka kasheta kuma suka kona ta. Addinin musulunci bai bada dama ga musulmi ya zagi ko wane Annabi daga Annabawan Allah ba, dan haka akwai bukatar shugabannin kiristoci su dauki aniyar wayar da kan mabiyansu akan illar taba mutunci ko zagin fiyayyen halitta wanda hakan ka iya tayar da husuma a cikin kasa.

Shugaban IZALA Sheikh Bala Lau ya kuma yi kira ga jama’a a duk lokacin da irin haka ya faru idan an kama wanda yayi zagin babu wani wanda yake da hakkin zartar wa wani haddi ko hukunci akan tuhumar da ake masa, har sai an gabatar da shi gaban alkali, shi ne wanda zai iya tabbatar masa da wannan laifin ko ya wanke shi.

“Al-Imam An-Nawawi: “Babu wanda yake da hurumin tsayarwa da mutane masu ‘yanci haddi sai shugaba, ko wanda shugaba ya nada, domin babu wanda ya taba zartar da hukuncin haddi akan wani a zamanin manzon Allah (S.A.W) sai da izininsa. Haka abin yake a zamanin halifofinsa duka. Saboda tsayar da haddi wani abu ne da yake bukatar zuzzurfan ilimi, kuma za a iya yin zalunci a cikinsa, don haka bai halatta ba sai da izinin shugaba”. [Al-Maj’mu’, juz’i na 20, shafi na 34].

Al-Imam Al-Kurtubi: “Babu sabani tsakanin malamai cewa, haddin kisa, babu wanda yake da hurumin tsayar da shi sai shugabanni. Su ne aka dora musu wannan alhaki a wuyansu”. [Tafsirinsa, Bakara, aya ta 187].�A wani gurin yana cewa, “Malaman fatwa sun yi ittifaki kan cewa, ba ya halatta ga wani ya yi wa wani haddin kisa, in banda shugaba. Mutane a junansu ba su da wannan hakkin. Wannan hakkin shugaba ne ko wanda shugaba ya nada”. Tafsirinsa, Bakara, aya ta 179.

Malam Ibn Rushd: “Malamai sun yi ittafiki cewa, shugaba ne kadai yake da hakkin tsayar da haddi” Bidayatul Mujtahid, juz’i na 4, shafi na228.

Don haka dole ne jama’a su fahimci, kuma su fahimtar da cewa, wannan aiki da wasu suka dauka ba koyarwar musulunci ba ne, kuma ba wani malami na musulunci da ya taba fatawar aikata irin wannan aika-aika da sunan son Annabi (S.A.W), ko kishin musulucni, kuma musulunci yana tir da irin wannan ta’asa a duk inda aka yi ta.

A karshe shehin Malamin yayi kira ga hukumomi Kira ga hukumomi da kan daukan mataki domin hukunta masu irin wannan laifi da gaggawa don toshe kafar hana irin wannan saboda masu daukan doka a hanu.
Allah ya ganar da mu. Amin.

JIBWIS NIGERIA

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button