AddiniUncategorized

Na yi laifi, kawai ku hukunta ni – Malam Abduljabbar

Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana cewa, Indai ba za a dubi Ubangiji ba, to kawai a hukunta shi yayi laifi.
Malamin ya bayyana hakan ne, yayin da yake amsa tambayar da Malam Kabir Bashir Abdulhamid ya yi masa.
Kamar yadda Freedomfm na ruwaito. Malamin ya ce, waɗannan matsalolin ba nasa ne shi kaɗai ba, batutuwa ne da aka ci zarafin addini, wanda shi kuma yake ƙoƙarin korewa.
Malam Abduljabbar ya ci gaba da cewa, yayi zaton za a yi wannan zaman ne da gaskiya saboda kishin Manzon tsira, amma abin ba haka bane.
Tun zagaye na biyu, ya zargi shirin muƙabalar da zalunci, inda Kwamishinan addini ya yi masa jan kunne.
Sai dai ya ƙara tabbatarwa yana mai cewa, akwai zalunci a cikin tsarin zaman.
Malam Abduljabbar ya ƙara da cewa, wannan matsalolin suna ta haifar da ridda a duniyar musulunci, mutane na barin musulunci ba adadi a duniya.
A don haka yake roƙon Malaman da su ji tsoron Allah a tsaya a duba lamarin daki-daki don a ceci musulunci.
Malamin ya kuma ce, kusan litattafai 500 ya zo da su, amma ya ga abin ba zai yiwu ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA