Addini

Darasi daga Rasuwar Abba Kyari! – Prof Mansur Sokoto

✍️ Mansur Sokoto
Assabar 24 ga Sha’aban 1441H (18 ga Afril 2020)

Babu shakka rasuwar wannan bawan Allah ta kidima ni matuka.
Mutum ne ba mai yawan magana ba. Masu sukar sa da masu yabon sa duk ba su iya kawo kalaminsa. Yau da gobe za ta bayyana alherinsa ga Najeriya ko Sharrinsa.

Muna yi masa fatar alheri; ya mutu Musulmi kuma a Jum’ah babbar rana. Sannan ya mutu a sanadiyyar Annoba wadda Annabi (S) ya ce, Allah yakan mayar da ita Rahama ga mumini.

Yanzu dai ta kara tabbata; wannan Annoba gaskiya ce. Ko mu dauki matakan da suka dace ko kuma mu yi da-na-sani a nan gaba.

Hasashen da Turawa suke yi ma nahiyarmu ta Afrika shi ne za ta zama cibiyar wannan annoba ta duniya in da Miliyoyin mutane za su mutu a sanadiyyar ta kamar yadda ya taba faruwa a kimanin shekaru 102 da suka wuce. Muna da hanyoyi biyu na hana aukuwar haka:
1) Dagewa ga addu’a tare da sadaka (Maganin musiba).
2) Daukar matakan kariya da masana suka ayyana, musamman kulle garuruwanmu kuf, sannan mu kula da tsaftar jiki da ta muhalli da nisantar taruwar jama’a wuri guda.

? Shawarata ga Malamai da Shugabannin kungiyoyin addini, don taimakawa wajen dakile yaduwar wannan cuta ita ce, a dakatar da Sallolin Tarawihi a azumi mai zuwa. Haka su ma majalisan Tafsiri a duk fadin kasar nan. A maimakon haka ayi amfani da kafofin sadarwa don isar da sakon Allah ga mutane.

In da ba a sanya dokar hana fita ba mutane su saurara ma musabaha da hannu, kuma su rage cushewa a wuri guda a Masallaci da Kasuwa da ko ina.

?️ Mu tuna, Allah _subhanahu_ ya ce: *”Ya ku wadanda suka yi imani ku rika yin hattara da sauna”* Suratun Nisa’i: 71. Don haka, mumini shi ne wanda yake riko da sababi sannan ya dogara ga Allah.

Allah ya jikan Abba Kyari da duk Musulmin da suka rasa rayukansu a cikin wannan annoba, ya sa ta zama rahama a gare su. Allah ya yaye ma duniya wannan musiba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button