AddiniLabarai

Wallahi Almajiri Daya da Allonsa yafi kannywood da abunda ke cikinta baki daya daraja a wajen Allah – Sheikh kasim abdullahi damagun

Malam kasim Abdullahi damagun yace wai yanzu wata yar fim tayi magana a daina haihuwar yara ana barinsu akan titi suna yawon almajiranci kuskure ne ta fadi wannan magana da ita da su wane ne iyaye suka san muhimmancin diyansu

Malam ya kara da cewa babu Komai A Kannywood In Banda Iskanci Da Fasikanci, Wallahi Almajiri Guda Daya Da Allonsa Yafi Kannywood Da Abunda Ke Cikinta Baki Daya Daraja A Wurin Allah.

Miye a cikin kannywood bancin iskanci da fasikanci wane dare ne jemage bai gani ba kawo kana surutu bakaje ka taimakesu ba,bakaje inda malamansu ka taimakesu ba kazo kana surutun banza a cikinsu ne ake samun mhaddata Alkur’ani a cikinsu ne ake samun gwani gwani da ake samu a Nigeria duk da ina sunka taso.

Da almajiranci karya ne da za’a samu wadanda gwani gwani a cikin Nigeriya ne ?.

Ga bidiyon nan da shafin mu koma tsangaya sunka wallafa bidiyon malamin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button