AddiniLabarai

Prof Ibrahim Maqari Ya Maka Dr Abdallah G/Kaya A Kotu

 Prof Ibrahim Maqar Ya Maka Dr Abdallah G/Kaya A Kotu
Prof Ibrahim Maqar Ya Maka Dr Abdallah G/Kaya A Kotu

Daga karshen al’amari Sheikh Professor Ibrahim Maqari babban Limamin Masallacin juma’a na kasa dake Abuja, Ya shigar da karan ‘dan uwansa Musulmi Malami Sheikh Dr Abdullahi Usman Gadon Kaya Kano a kotun Musulunci a dalilin batanci kamar yadda majiyarmu ta samu wannan labari a shafin Datti Assalafy
Sheikh Ibrahim Maqari ya zargi Sheikh Abdullahi Gadon kaya da laifin bata masa suna kamar haka:
1- Malam Abdallah yace Malam Maqari Makiyin Sunnar Manzon Allah (SAW) ne
2- Malam Abdallah yace Malam Maqari duk lokacin da Malamai sukayi wa’azi sai ya kalubalanci wadannan Malamai
3- Malam Abdallah yace Malam Maqari duk lokacin da wasu miyagu sukayi batanci wa Manzon Allah (SAW) sai ya fito ko a boye ko a fili ya karesu
4- Malam Abdallah yace Malam Maqari ya shahara wajen kalubalantar masu kare martaban Manzon Allah (SAW)
5- Malam Abdallah yace wasu matasa sunyi batanci ga Annabi (SAW) Malam Maqari yasa an saki matasan
6- Malam Abdallah yace Malam Maqari makiyin addinin Musulunci ne
7- Malam Abdallah yace Malam Maqari yana kare duk mai zagin Annabi (SAW) Prof Ibrahim Maqar Ya Maka Dr Abdallah G/Kaya A Kotu Prof Ibrahim Maqar Ya Maka Dr Abdallah G/Kaya A Kotu
 Prof Ibrahim Maqar Ya Maka Dr Abdallah G/Kaya A Kotu
Wadannan sune manyan tuhuma guda 7 wanda Sheikh Ibrahim Maqari yake yiwa Sheikh Abdallah a kotun Musulunci, ya bukaci Sheikh Abdallah ya fito ya karyata kansa a manyan kafofin watsa labarai, sannan ya biyashi diyyar kudi Naira Miliyan 20 na bata suna
Hakika ni Datti Assalafiy banji dadin faruwar wannan al’amari ba, wannan sabanin ya faru ne a dalilin wakilin iblis shugaban zindikai na jihar Kano Abduljabbar Nasiru Kabara (L)
Ina ganin kima da mutuncin wadannan Manyan Malamai guda biyu, kuma dukkanninsu suna da amfani a cikin al’ummar Musulmi duk da akida ta banbanta a tsakaninsu, amma banso ace wannan sabanin ya kai ga tafiya kotu ba
Tun da nake a rayuwata ban taba ji Malamin addinin Kirista yayi karan ‘dan uwansa Malamin addinin Kirista ba, kuma suna samun sabani da cin amana sosai a tsakaninsu, amma duk shari’arsu a sirrance sukeyi a tsakaninsu ba wanda ya sani
Wannan abinda ya faru tsakanin Malam Maqari da Malam Abdallah ya sake fito da mummunan rashin shugabanci da rabuwa da rashin hadin kai dake tsakanin Musulmai a Nigeria, hakan ba zai haifar da komai ba sai koma baya da kyamar juna a tsakanin Musulmai
Allah Ya sauwake, Allah Ya sasanta tsakaninsu Amin

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA