Labarai

Kwamishina a Kano yayi murna da rasuwar Abba Kyari

Advertisment

Kwamishinan dake Lura da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano, Engr. Muazu Magaji ya nuna farincikinsa da rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

A rubutu da ya dinga yi na nuna farincikinsa, a ranar Asabar, Muazu Magaji ya bayyana cewar “Abin Garin ciki guda biyu, Najeriya ta kubuta, Abba Kyari ya mutu da Annoba”.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar shi bai iya munafurci ba, dan haka dole ya fito fili ya nuna farincikinsa kan rasuwar Abba Kyari, a cewarsa.

Mutane da dama cikin da wajen jihar Kano suka kalubalanci wadannan kalamai na kwamishinan da yayi akan Abba Kyari, inda wasu ke kira ga Gwamnan Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da ya koreshi daga mukaminsa saboda cin amana ne abinda yayi.

Har ya zuwa lokacin hada Wannan rahoto, Engr. Muazu Magaji na cigaba da yin kalamai na nuna murna da farinciki kan rasuwar, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Madogara : Nijeriyarmu a yau

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button