Kannywood

A Yanzu Burina Shi Ne Na Samu Miji Na Yi Aure – Teema Makamashi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Fitacciyar jaruma Fatima Muhammad Isah Yola wadda aka fi sani da Teemah Makamashi, ta bayyana muradin ta na samun miji Wanda hakan zai ba ta dama ita ma ta je ta huta bayan gwagwarmayar da ta sha a harkar fim, kafin Allah ya daga ta ta zama babbar jarumar da a yanzu ake ji da ita a masana’antar finafinai ta kannywood.

Teemah Makamashi ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu a game da irin nasarorin da ta samu a matsayin ta na babbar jaruma, in da ta fara da cewar ” Kafin na samu daukaka duniya tasanni na sha gwagwarmaya sosai a cikin masana’antar fim , amma a yanzu abin ya zama tarihi sai dai godiya ga Allah musamman idan na kalli irin dunbun nasarorin da na samu  wannan kuma abin alfahari ne a gare ni.

Mun kuma tambaye ta game da kallon ta da ake yi a matsayin jaruma mai aji Wanda hakan ya sa ake shayin ta idan za a kira ta aikin fim sai ta ce ” To ai aji daban Sana’a daban, kuma mutunci  ne ya ke jawowa mutum haka.

domin na mutunta kaina ne ya sa ake shakka ta  don na san na gaba da ni , duk Wanda yake dama da ni zan ba shi matsayin sa , idan kana sa’a na zan ba ka matsayin ka , ina ganin hakan ne ya sa ake ganina a matsayin mai aji.

Daga karshe ta bayyana mana burin ta in da take cewa ” A yanzu buri na shi ne na samu miji na yi aure nima na je na huta a gidan miji na don haka ina rokon Allah ya kawo mini miji nagari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button