Shin da Gaske Hamisu Breaker yayi aure asirance ?
Shin Ko Kun San Cewa Mawaƙi Hamisu Breaker Ya Yi Aure Watanni Bakwai Da Su Ka Wuce ?
Wata sabuwa inji yan chacha yanzu nan majiyarmu tayi kicibis da wani labari nai mai ban mamaki wanda abun akwai daure kai irin yadda ake hidima da rakashewa wajen auren jaruman masanantar kannywood ko mawaka amma ace haka hamisu breaker yayiwa mutane ga abinda dokin karfe tv sunka ruwaito.
Labarin da ke shigowa Ofishinmu na Jaridar Dokin Ƙarfe TV da ɗumi-ɗumi yanzu-yanzu, wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa fitaccen mawaƙin Hausa, Hamisu Breaker Ɗorayi ya yi aure cikin sirri tsawon watanni bakwai da su ka wuce.
Hamisu Breaker, babban mawaƙi ne mai rere waƙoƙin soyayya masu ratsa zuciya cikin harshen Hausa, wanda ko da a ƴan kwanakin da su ka gabata an yi ta cece-ku-ce akansa biyo bayan wasu kalamai da abokiyar sana’arsa wacce ta ke taka rawa cikin waƙensa, Rakiya Musa ta yi cikin hira da Hadiza Gabon inda wasu ke zargin cewa da Hamisu Breaker ɗin ta ke irin yadda ta siffanta tsananin soyayyar da ta ke yi wa wani mutum tun kafin ya samu ɗaukaka.
A binciken da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta gudanar ta gano cewa tabbas Hamisu Breaker ya yi aure a wani yanayi mai kama da sirri tayadda hatta abokan sana’arsa a masana’antar Kannywood ba kowa ne ya sani da auren ba sai ƴan ƙalilan.
Shin ko mai ya sa babban jarumin mawaƙi kamar Breaker ya yi aure cikin sarri duk da irin ɗaukaka da shuhurar da ya ke da ita ?, Shin masu karatu mai za ku ce ?
Bayan wannan bincike da dokin ƙarfe tv bamu yi kasa a gwiwa ba shine munka kara zurfafa bincike inda majiyarmu hausaloaded ta samu tabbacin gaskiya wannan lamari daga abokin sana’ar sa inda ya shaidamin cewa tabbas yayi aure wannan zance da gaske ne.