Kannywood

Abba Gida Gida Ya Nada Fauziyya D Suleman Ssa

Advertisment

Maigirma Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya nada shahararriyar mai aikin Jin Kai wadda tayi fice wajen nemawa mutanen da suke fuskantar matsin rayuwa taimako.

Hajiya Fauziyua wadda ta kasance shahararriyar marubuciyar Hausa an santa a duk fadin Arewacin Najeriya a kan aikin taimakon al’uma musamman wadanda suka samu kansu cikin halin kakani kayi. Wannan nadi abin a yaba me da yazo cikin bazata musamman ganin cewa Ita ba yarsiyasa bace.

Tuni dai wakilin Gwamnan ya mika mata takardar da shi kansa gwamnan ya rubuta da hannunsa wadda take tabbatar da nadin nata a matsayin babbar mataimakiya ta ga Gwamnan ta fuskar taimakon mabukata da gajiyayyu.

Mai baiwa Gwamna shawara na musamman a masanantar kannywood shine ya kawowa Fauziyya D Suleman wannan nadin da ankayi mata.

Advertisment

Abba Gida Gida Ya Nada Fauziyya D Suleman Ssa Abba Gida Gida Ya Nada Fauziyya D Suleman Ssa Abba Gida Gida Ya Nada Fauziyya D Suleman Ssa

Sakon da Mataimakiya  SSA Fauziyya D Suleman ta Gwamna Abba Gida ta wallafa kenan a shafinta na sada zumunta da godiya.

ABUN KAMAR DA WASA
Dazu wani ya kirani ya gaya mun suna meeting da mai girma Gwabnan Kano Abba Kabir Yusif, ya yi ta ambaton irin aikin da na ke yi saboda yana bibiyar shafina, ya ce tabbas kina abu mai kyau ki ci gaba na yi godiya
.
Da laasar kuma sai abokin aikina Nasir Nid ya shigo office yana dariya ya ce Uwar marayu mai girma gwabna ya baki mukami akan aikinki na jinkai, na ce tsokanata ka ke ya yi, ya yi ta rantsuwa muna dariya.
Zuwa can sai ga kiran Sunusi Oscar ya ce mun hajiya Fauziyya mai gurma Gwabna ya baki mukamin SSA, na ce ni kuma, ya ce eh yanzu haka muna meeting da shi zan kira ki idan mun kammala, zuwa can ya kira ya ce mu hadu.

Bayan mun hadu ya bani takardarnan ya ce mai girma Gwabna ne ya ce a baki, na rike baki da mamaki na ce ni da ba yar siyasa ba yaya zaa bani mukami, sai ya ce eh ai daman ba akan siyasa aka zabe ki ba, mai girma Gwabna ya baki mukami akan aikin da ki ke yi na tallafi da jinkai domin yana ganin aikinki yana bin fejinki hankalinsa yana tashi akan duk abun da ki ke sakawa, ga takardar ki amsa.
Na amshi takardar na kalla, na ce yanzu wannan daga hannun gwabna ta ke, ya ce kwarai kuwa duk Kano wa ya isa ya yi rubutu da jan biro idan ba gwabna na.

Kamar dai yadda ku ke ganin wannan takarda mai girma Gwabnan Kano ya bani mikamin SENIOR SPECIAL ASSISTANT NEEDY AND VULNERABLE, ina godiya kwarai da gaske ga mai Girma Gwabna.
Ina neman addu’ar ku bisa wannan nauyi da Mai girma Gwabna ya dora mun yan’uwa, Allah ya sa ya zama alkairi ga al’ummar jahar Kano, Allah ya bani ikon cinye jarrabawar da ke tattare da wannan nauyin Amin ya Allah.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button