Labarai

Dakarun Nijeriya sun sake samun nasarar hallaka kasurgumin dan fashin daji a Katsina

A wata babbar nasara a yakin da ake yi da ta’ddanci, an kashe kasurgumin dan fashin dajin nan, Sani Wala Burki wanda ke addabar kananan hukumomin Safana da Batsari a jihar Katsina.

Kafar yada labarai mai kawo rahoton tsaro a Arewa, Zagazola Makama ce ta rawaito cewa jami’an tsaro da ‘yan banga na sa kai a jihar Katsina ne suka hallaka dan fashin dajin tare da mayakansa.

Lamarin ya faru ne a daren jiya a yayin ‘yan bindigar suka yi yunkurin kai hari ga mazauna garin Safana.

A martanin da suka mayar ‘yan bindigar da suka samu hadin kai da jami’an tsaro sun fuskanci ‘yan bindigar.

Acewar mazauna garin, an kashe Burki da mayakansa da dama a yayin fafatawar.

Sani Wala Burki dai ya shahara wajen kai hare-hare a yankin.

Hakan na zuwa ne bayan sojojin Nijeriya sun kashe kasurgumin dan fashin daji, Kachalla Sububu a jihar Zamfara.

Majiya: Zagazola Makama mai sharhi kan lamuran tsaro a yankin yammancin Afrika.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button