Labarai

Kyakkyawar mage ta kammala karatun digiri tare da mai ita, makarantar sun taya ta murna

Francesca Bourdier tana da wata kyakkyawar mage wacce take zama tare da ita duk lokacin da take da aji a manhajar Zoom, lokacin tana ɗaliba a jami’ar Texas a birnin Austin.

Dukkanin su sun samu kwalin digiri a fannin cigaban ɗan Adam da kimiyyar iyali.

A hakan, magen ta halarci kowane aji. Hakan ya sanya Francesca jin cewa magen ta cancanci ta kammala karatun lokacin da ranar bikin kammala makarantar ta zo.

Jaridar Legit.ng da LIB sun rahoto cewa, Francesca ta shaida wa tashar labarai ta Fox7 cewa a dalilin ɓarkewar annobar cutar korona, mafi yawa daga cikin lokutan da ta kwashe a makaranta, ta yi su a gida ne, inda take ɗaukar karatu ta hanyar amfani da manhajar Zoom.

Makarantar ta aike musu da saƙon taya murna

Sai dai magen ta, mai suna Suki ta zama yar ajin ta kuma wacce su ke karatu tare inda ta halarci kowane aji.

Francesca ta rubuta labarin su a shafin Instagram inda take cewa:

 

Tabbas mage ta, ta halarci duk lakcar da nayi a manjahar Zoom, saboda haka a tare zamu kammala karatun mu daga jamiar Texas, a birnin Austin

Tuni har jami’ar ta taya wannan mage murnar kammala karatun ta bayan labarin ya karaɗe yanar gizo.

Mutane sun taya magen murna

@sabihayounus_  ya rubuta:

Na ganku a labarai, hakan ya faranta min rai sosai, ina taya ku murna.

@katts_meow ya rubuta:

Ikon Allah!! Wannan babban lamari ne. Ina taya ku murna.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button