Datti Assalafy yayi Martani Akan yadda Muneerat tayi Nadamar Bari da karuwancin da tayi yanzu ta zamo Gwanjo
Fitaccen marubucin nan a shafin sada zumunta Datti Assalafy wanda a lokutan baya shine wanda yayi ta yiwa wannan baiwar Allah nasiha amma tayi babu ajiyarsa babu irin kalamai na zagi da cin mutuncin da baya yi masa ba kwatsa sai ga ta tana damar abubuwan da tayi inda shi kuma yayi rubutu Shsfinsa kamar haka.
“MUYI HANKALI DA YAUDARAN DUNIYA
إِنَّا لِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ
Idan ance Muneerat Abdussalam a kafofin sada zumunta musamman Facebook da YouTube an santa, tayi fice wajen yada abubuwan da suke ruguza tarbiyyan yara tare da koya musu batsa da k@ruwanci
Sunan Muneerat ya fito sosai a duniya lokacin da Datti Assalafiy yayi karambatta da ita, har nayi kira ga ethical hackers su zo mu tare mu lalata kafofin da take yada batsa a wancan lokaci
Muneerat Abdussalam babu irin zagi da tsinuwar da bata yiwa Datti Assalafiy ba saboda kawai na bata shawara, a tsammaninta Datti Assalafiy makiyin ta ne
‘Yan duniya sun yaudari Muneerat, sukayi ta zugata tana yin abinda ta ga dama, kowa ya san irin rigimar da mukayi da ita a lokacin
Har na fara mantawa da labarin Muneerat, sai gashi jiya ana ta mentioning sunana a karkashin posting da tayi har da wanda tayi yau, sai yanzu na samu lokaci na karanta halin da Muneerat ta shiga
Kamar yadda zaku gani a hoto, Muneerat ta saki hotunanta dake bayyana rashin lafiya da ya kamata, sannan duka masoyanta masu zugata sun gujeta kamar yadda ta fada
Na kalli hoton Munirat da kyau, da alama jinyar Kansa ce ta kama idonta, jinyace mai wuyar magani, ban taba ganin wanda ya kamu da jinyar yana da karamin karfi ya wanye lafiya ba, Tsakanina da Allah na tausayawa Muneerat, hakika ta hadu da jarrabawa mai girma da ban tsoro
Abu daya ne ya bani mamaki shine yadda masoya da abokan huldar Muneerat suka gujeta bayan ta hadu da wannan jinya, basu kyauta mata ba gaskiya, kuma wannan shine abinda muka jima muna bayyanawa zai faru da irin wadannan mata da suka rungumi yaudaran duniya
Muneerat bata da kowa, bata da aure balle mijinta ya kula da ita, bata da ‘ya’ya balle su kula da ita, ‘yan duniya ta kama a matsayin masoya kuma gashi sun gujeta, gashi nan tana nadamar munanan abubuwa da ta aikata a rayuwarta
Ina tunatar da Muneerat ta fahimci cewa tana da sauran lokacin tuba tare da komawa zuwa ga Allah, a Musulunci ba’a yanke tsammani daga samun rahamar Allah (T)
Shikenan fa duniya ta sallami Muneerat daga yayi, wannan ya zama darasi garemu gaba daya, tabbas muyi hankali da yaudaran duniya
Muna rokon Allah Ya yafe wa Muneerat, Allah Ya kawo mata dauki ta inda batayi tsammani ba”