Labarai

Gwamnan jihar Edo, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar daga N40,000 zuwa N70,000 – Godwin Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikata a jihar daga N40,000 zuwa N70,000.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da sabuwar katafaren sakatariyar ma’aikata da aka gina na kungiyoyin kwadago a jihar, a kan titin Temboga, Ikpoba-Hill, a cikin birnin Kamar yadda majiyarmu ta ruwaito daga Dclhausa.

Wani Labari: Dalilai huɗu da suka haifar da wahalar man fetur a Najeriya

‘Yan Najeriya na cikin damuwar matsalar manfetur, wadda tun shekaru suke fama da tsadarsa, amma yanzu ƙarancinsa ya ƙara ta’azzara lamarin.

A gidajen man gwamnati ana sayar da man ƙasa da naira 620, amma a wasu jihohin irin su Sokoto da Kano da Jigawa ana sayar da man har sama da naira 1000, kamar yadda BBC ta tabbatar.

A yadda mutanen ƙasar suka riƙa tsammani a baya, idan aka ƙara farashin man, za a same shi a wadace a kowanne gidan mai.

Sai dai wannan tunani ya saɓa da tunanin mutane. Domin kuwa ana fama da tsadar man kuma ga ƙarancinsa da ya dabaibaye ko’ina.

Shin waɗanne dalilai ne suka janyo tsadar, ta ya ya za’a iya magance wannan matsala? wasu daga cikin tambayoyin da BBC ta yi wa Bashir Ahmad Danmalan kenan shugaban ƙungiyar dillalan man fetur da Iskar Gas ta Najeriya.

1 Ƙarancin ƙananan jiragen dakon mai

2 Ƙarin kuɗin ruwa’

3 An ƙure mai saya da mai sayar da kayan

4 Zargin fasa-ƙaurin man a Legas’

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button