Labarai

Audu bulama bukarti yayi kira da babba murya, gwamnati ta gaggauta biyan N-power

Yakamata FG ta gaggauta biyan matasa N-power - Audu bulama bukarti

Babban lauya Audu bulama bukarti yayi kira ga gwamnatin tarayya akan alawus da ake biyan matasa Naira dubu talatin wanda suke biyar bashi watanni 9 zuwa 12.

Bulama bukarti yayi wannan kira da babba murya a yau din a shafinsa na sada zumunta inda ya wallafa.

“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta biyan matasan N-Power alawus dinsu na watanni 9 zuwa 12 da ba a biya ba. Biyan wadannan matasa wannan kudi zai iya ba su dama su kama sana’o’in da za su rufa kansu asiri, harma su dau wandansu aiki, kuma su tallafawa iyaye da yan’uwa, in shaa Allah. Hakan zai iya rage tsananin rayuwar da ake ciki, ya kuma tallafawa tattalin arzikin kasa.”

Tabbas wannan kuɗin alawus suna da matuƙar amfani a dai-dai irin wannan lokaci domin kudi ne da zasu kai masu yawa da za’a iya amfani da shi wajen kama sana’o’i daban daban da zasu taimaki rayuwar su.

Wani labari na daban : Gwamnan jihar Edo, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar daga N40,000 zuwa N70,000 – Godwin Obaseki

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kara albashi mafi karanci ga ma’aikata a jihar daga N40,000 zuwa N70,000.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da sabuwar katafaren sakatariyar ma’aikata da aka gina na kungiyoyin kwadago a jihar, a kan titin Temboga, Ikpoba-Hill, a cikin birnin Benin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button