Zaman lafiya ya dawo a kananan hukumomi 13 na jihar Katsina – Gwamnati


Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Alhaji Faruq Lawan Jobe, ya ce gwamnatin jiha ta yi kokari ta maido da zaman lafiya a kananan hukumomi 13 cikin 22 da ke fama da matsalar tsaro a jihar.
Jaridar This day ta rawaito cewa Faruq Jobe na magana ne a gaban ‘yan jarida, inda ya ce an samu wannan nasarar ne ta dalilin ayyukan jami’an sa kai na ‘Community Watch Corp’ da gwamnatin ta kirkiro, hadin guiwa da sauran jami’an tsaro a jihar.
Daga cikin kananan hukumomin da tsaron ya fara inganta, a ta bakin mataimakin Gwamnan jihar, akwai Batagarawa, Dutsinma, Bindawa, Kusada, Funtua, Danja, Bakori, Malumfashi, Kafur, Musawa, Ingawa, Charanci da Matazu.
Wani labari : Ɓarayin Daji A Birnin Gwari Sun Sha Ruwan Wuta Wotowoto
Rundunar sojin Najeriya ta 1 division Kaduna tayi nasarar ragargazar ƴan ta’addar daji a ƙananan hukumomin Igabi da Giwa a Birnin Gwari na jihar, sun kuma samu makamai da Alburusai.
Maharan a yankin Maganda-Dausayi – Mugaba sun kai harin ƙwanton bauna ga Jami’an tsaron yayin da suke aikin sintiri, inda suka yi musayar wuta, take Jami’an tsaro suka maida martani
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



