Wasu Abubuwan Da Mata Gajeru Suka yiwa sauran mata zarra da su – Binciken Masana
Wani ma’abota ci amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Ustaz Usman inda ya zan zankado wasu muhimman abubuwa da Allah ya baiwa gajerun mata wanda dogayen mata basu da.
Duk da ana zolayar su da cewa doguwar mace duniya ce ashe ba’a nan gizo ke sakar ba sai kaji irin alfanun da Allah ya baiwa gajerun mata nan zaka ƙara tabbatar da hallitar Allah ni’ima ce.
Yar kurkura Da injin Daf, Yar karamar kasa da Arzikin Man fetir. Da sauransu sune kirari da kambamawa da ake yiwa Gajerun mata.
Duk da dai yawan mutane ma basu san meye dalilin da ake musu Wannan Kirarin ba.
A Darussanmu na baya mun kawo fa’idojin da wasu daga cikin baiwa da Allah yawa nau’ikan mata da muke tare dasu. Kamar Su Doguwa, siririya yar duma duma da wasunsu.
Yau kuma zamu Dan fadi wasu abubuwa da gajerun mata suke dasu, wanda suka yiwa sauran matan shal dasu.
1- Tsufa:- shekaru basu cika nuna Mace gajeriya ba da wuri, ita kadaice macen da take cin zamani da yawa ba tare da mutane Sun gano ta ba.
Gajeriya tana iya zamani da sa’anninta ta kuma shiga cikin yayyenta kana ta dawo cikin kannita ta saje dasu sak ba tare da mutane Sun gane ba.
2- Kwalliya:- 75% daga cikin Gajerun mata naturally yan kwalliya ne. Saboda sun kasance suna son a ko da yaushe ace sune a sama da kowa. Shi yasa suke dagewa suyi iya yin su domin ganin Sun kasance a koda yaushe tsaf tsaf dasu.
3- Wadataccen Kirji da kuma baya :- Wannan kam kusan abune wanda yake a filin, domin kuwa anyi iftifa’in cewa a duk mata gajeru Goma zaka samu bakwai daga ciki suna dauke da wadataccen Dukiyar Fulani da mazaunai. Shi yasa har wasu suke cewa tsawon da basu dashi duk a chan aka tare musu.
4- Cikakkiyar Lafiya :- Bincike ya tabbatar da cewa duk cikin nau’in mata to fa gajeru suke da karancin yin rashin lpy da laulayi ko kasala.
5- Lafiyarsu wajen jima’i:- Masanin ilmin jima’i Sun tabbatar da cewa mata gajeru suna daga cikin mata masu dauriya da juriya a yayin gudunar da rayuwar auratayya.
Kazalika suna da dandano na musamman da zai wuyar gaske ga namiji yaji Sun gimshe shi da wurwuri, kuma basu cika neman ruwan ni’ima su rasa ba yayin gudanar da jima’in.
Masanan suka ce duk cikin nau’in mata akan same su da ni’ima ne yayin gudanar da wasannin motsa sha’awa da kuma round din farko.
Za’a cigaba …….