Ceto Kasa: Lokaci ya yi da za a koma a sake tsari, shugabanni sun gaza a Najeriya -Kungiyar Dattawan Arewa


Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ta bayyana cewa lokaci ya yi da za a koma kan teburin dubi domin ceto Najeriya.
Shugaban taron, Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana haka a wajen gabatarwa da kuma kaddamar da littafin ‘Kotu da Siyasa’ wanda Dr Umar Ardo ya rubuta a Abuja.
Ya jaddada cewa ba lokaci ne na nuna yatsa ba, sai dai a koma inda Najeriya ta dace.
Jaridar liberty na ruwaito cewa ya sake jaddada kiransa na samar da tsarin gwamnati na majalisar dokoki, yana mai bayyana tsarin mulkin shugaban kasa sama da shekaru 24 a matsayin “tsarin da ya gaza” ga Najeriya.
“Lokaci ya yi da za mu koma kan allon zane, domin a ceto kasar nan. Mun yi kasa a gwiwa sosai kuma wannan dole ne a daina. Mun gaza kanmu kuma ba mu da dalilin yin korafi.
“Musamman a siyasance, ba mu da dalilin yin korafi. Wannan taron a gare ni wata dama ce da za mu tattauna da kanmu game da gazawar da muka yi a kasa baki daya
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




