Labarai

An sake sakin wani faifan bidiyon mutane da anka sace a jirgin kasan kaduna

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjoji bayan tayar da bam a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, sun fitar da sabon bidiyo, inda a cikin wadanda ake tsare da su aka hango har da wani dan kasar waje.

Sun fitar da bidiyon mai tsawon minti biyu ne ranar Lahadi, inda aka gano su dauke da makamai, suna tilasta wasu daga cikin fasinjojin su yi magana. Jaridar Aminiya ta wallafa

Sai dai daga wadanda aka yi garkuwar da su, an ga wani mutum da aka yi ittifakin dan nahiyar Asiya ne.

A cikin bidiyon dai, ya tsaya a gaban kyamara, kafin daga bisani ya koma cikin wadanda aka yi garkuwar da su da ke zazzaune a kasa.

Daya daga cikin wadanda aka sace din da ke sanye shudin wando, wacce dalibar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ce, ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta ceto su.

“Ina magana ne da yawun sauran daliban da suke a nan. Gwamnati ta taimaka ta ji kokenmu, ta kawo mana dauki,” inji ta.

Daga nan ne sai aka ji wata muryar wani yana tambayarta a ina take karatu, inda ta amsa da cewa KASU.

Sai ya tambayeta me take karanta, inda ta ce Fannin Aikin Gona.

Ita ma wata daga cikin wadanda ake tsare da su din wacce ta ce sunanta Gladys Tony, ta ce tana aiki ne da Kamfanin Kera Makamai na Sojoji da ke Kaduna.

Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin ci gaba da aiki tukuru wajen ganin ta ceto mutanen.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button