Za’a Samu Daidaiton Farashin Sukari da Sauran kayayyakin Masarufi Kafin Watan Ramadan – Ministar Kasuwanci
Ministar masana’antu, Kasuwanci da zuba jari, Dr Doris Uzoka-Anite, tace manyan matatun mai a fadin kasar nan sun ba ta tabbacin tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki a Najeriya
Ta Kuma bayyana Cewa sun bata tabbacin cewa ba za a kara farashin sikari ba a cikin watan Ramadan
Sun bayar da wannan tabbacin ne ta wata sanarwa a jiya Talata a Legas mai ɗauke da sa hannun Tolu Moyan, Mataimakin na Musamman kan Harƙoƙin yada labarai ga Ministar masana’antu, Kasuwanci da zuba jari.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, watan Ramadan mai alfarma, lokacin da musulmin duniya suka sadaukar da azumi da addu’o’i, an tsara shi ne daga 10 ga Maris zuwa 9 ga Afrilu, 2024.
Yawanci A lokacin Farashin sukari da wasu kayan masarufi suna tashin Gwauron zabi Saboda dokar buƙata fiye da wadata.
A Cewar sanarwar, Ministar Ta ziyarci manyan masu samar da kayan masarufi irin su Dangote Sugar Refinery Plc, BUA Sugar Refinery Ltd., Flour Mills Ltd., Bestaf Ltd., Golden Sugar Company, da Coca Cola Hellenic Bottling Company (CHBN).
Ministar Ta bayyana cewa matakin yayi daidai da ajandar Gwamnatin Tarayya na samar da abinci da daidaita tattalin arziki.