Labarai

Abin sha’awa kalli Zafaffan Hotunan Ango Tare Da Amaryarsa Sanye Da Niqabi A wajen Biki

Wani matashin mai amfani da shafin Twitter, @kampo_k, ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ya wallafa hotuna don jinjina wa sabuwar masoyiyarsa.

A wani sako da ya wallafa a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, sabon angon ya ce ya yi auren ne da burin ransa a ranar karshe ta watan Afrilun shekarar 2020.

Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi Hoto: @kampo_k
Hotunan bikinsa masu ban sha’awa sun sa masu amfani da shafin Twitter da dama sun taya shi murna. Sai dai kuma, waɗanda suka yi tambayoyi, suna son sanin dalilin da ya sa ma’auratan suka zabi yin irin shigar da suka yi.
Mutumin ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewa:

“A wannan ranar a watan da ya gabata wani kyakkyawan abu ya same ni. Alhamdulilah. Na kama masoyiyata a wannan rana.”


Tana da kyau. Ina taya ku murna.”
@SandraAdaeze4 ta tambaya:
Kada ku yi fushi,kawai ina so in sani don Allah. Don haka tambayata ita ce me yasa aka rufe fuskarta? Rigar ta yi kyau sosai.”
@horlardoyeen ya ce:
“Rigarta tayi kyau sosai.”
@AdemolaSolalu ya amsa:
“Wannan shine ainihin abin da wannan hoton yake nufin cimmawa. Ko da baka bayyana jikinka ba, kana iya zama kyakkyawa.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button