Labarai

‘Yan Arewa munafukai ne sun yi shiru saboda Musulmi dan Arewa ne yake mulki – Aisha Yesufu

Yar gwagwarmaya Aisha Yesufu ta yi wa ‘yan arewa wankin babban bargo ciki har da wasu masu yi mata tsokaci a karkashin wallafarta.
A cewarta, ‘yan arewa da dama ba su da abin yi sai lokacin zabe ya yi a dauke su kamar awaki don su kada kuri’a.
Aisha Yesufu ta ce bata ga wani amfanin shugabancin kasan dan arewa ba. Ta ce za ta yi bayani da kyau ne don duk wani dan arewa ya ji wa kunnensa kuma ya fahimta.
Jaridar Labarunhausa ta ruwaito cewa ta ce rashin tsaro yana lalata yankin arewa amma saboda munafunci irin na ‘yan arewa ba za su iya bude baki don su yi magana ba saboda dan arewa ne ya ke shugabanci.
A cewar Aisha Yesufu, lokacin shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya na karagar mulki babu dan arewan da ya san kaddara.
A lokacin duk wasu malamai da masallatai suka dinga fitowa su na cece-kuce , inda ta ce duk wata tsiya daga arewa ta ke farawa.
Ta ce talauci ya yiwa arewa katutu, a duniya kowa ya san yadda Najeriya ta ke fama da fatara kuma satar mutane a Najeriya ya fi sauki akan satan akuya.
Ta ce hanyar Abuja zuwa Kaduna ta zama bala’i ana satar mutane kamar me. Sannan malamai sun yi shiru sun ki yin magana, cewar Aisha Yesufu.
Aisha Yesufu ta ce matsawar mutane sun yi shiru da sunan addu’a suke yi ba tare da yin magana ba, ba tare da yi wa shugaban kasa bayani ba, ba a fara wahala ba a kasar nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button