Tonon silili : An sace Makudan kudi kinamin naira Biliyan 37.1 a karkashin tsohuwar minista,sadiya faruq


Cikakkun bayanai na binciken da ake yi na musamman da Jaridar PUNCH ta samu ya nuna cewa an fitar da kuɗaɗen ne daga asusun Gwamnatin tarayya kuma an tura su zuwa wasu asusun banki 38 daban-daban da ke cikin wasu bankunan kasuwanci na Gado guda biyar mallakar ko kuma alaka da wani dan kwangila, James Okwete.
Bayan samun kuɗaɗen, Okwete ya mikawa ‘yan Kasuwar canji N6,746,034,000.00, ya ciro tsabar kudi N540,000,000.00, ya siyo motoci na alfarma da N288,348,600.00, Sannan ya sayi Gidaje na alfarma a Abuja, da Jihar Enugu, da N12,510.0.00.
Kamfanoni 53 ne ake zargin Okwete ne, Wanda kuma aka ce sunyi amfani da 47 Daga cikin kamfanonin wajen dage kwangilolin da suka kai N27,423,824,339.86.
Haka kuma an danganta shi da asusun banki 143 a cikin bankunan Kasuwanci 12 inda asusu 134 asusun kamfanoni ne da keda alaƙa da kamfanoni daban-daban.
Wani labarin : Akwai bukatar a kama Buhari – Gudaji, mahadi shehu cikin wata hira ta musamman
A wata hira ta musamman da gidan jaridar Dclhausa na yi da gudaji kazaure da kuma mahadi shehu akan Emefiele, idan baku manta a zaman da ankayi na kotu an tabbatar da Emefile ya mallaki asusun ajiya wato akawon guda 593 wanda duk a kasashen waje wannan babu shakka wannan mutum ya azurta kanshi da kanshi da kudin al’umma.
A cikin wannan hirar zaku irin yadda gudaji kazaure yake cewa daman tun can a baya sun nunawa duniya cewa tabbas tsohon gwamnan babban bankin Najeriya shine matsalar tattalin arziki Nijeriya kuma gashi nan abun ya fito fili anyi walkiya ta haska.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




