Labarai

Babban Magana: An Kama Marubuciyar Littafin ‘Yadda Za Ki Kashe Mijinki’ Da Laifin Kashe Mijinta

Advertisment

Amurka – Wannan labarin na iya kama da shirin fim, amma da gaske ne, inda wata kotun Amurka ta kama Nancy Brophy – wata marubuciyar wani littafi, ‘Yadda Za Ki Halaka Mijinki’ – dumu-dumu da laifin halaka mijinta

A 2011, Nancy ta wallafa littafin wanda ta tattaro hanyoyi da dama wadanda mace za ta iya amfani da su wurin halaka mijinta ba tare da an gano ta ba, rahoton The Cable . Da legit na ruwaito

A watan Yunin 2018, an tsinci gawar mijin Nancy, Daniel Brophy, a Cibiyar Oregon Culinary, inda ya ke koyar da dalibai.

An ga yadda aka harbi Brophy sau biyu a bayansa.

Bayan bincike, ‘yan sanda sun zargi matarsa, wanda hukuncin laifin shi ne zaman gidan yari har karshen rayuwar mutum.Babban Magana: An Kama Marubuciyar Littafin 'Yadda Za Ki Kashe Mijinki' Da Laifin Kashe Mijinta

An gan ta a lokacin da aka yi kisan kusa da cibiyar da mijin ke koyarwa.

Nancy ta musanta zargin da aka yi mata.

Kamar yadda New York Times ta ruwaito, masu bincike sun gano wani bidiyonta a kusa da cibiyar da ya ke aiki yayin da ta ke tuka motarta kusa da wurin a daidai lokacin da aka yi kisan.

Yayin da aka tambayeta abinda ta ke yi a lokacin, mawallafiyar ta ce ba za ta iya tunawa ba, ta yiwu ta je shan shayi ko kuma yin wasu ‘yan rubuce-rubuce.

Yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun bayyana shaidar yadda Nancy ta siya bindiga ana saura watanni kadan da mutuwar mijinta kamar yadda The Cable ta nuna.

Nancy ta yi yunkurin boye duk wasu shaidu
Masu gabatar da karar sun sanar da kotu cewa mawallafiyar ta tabbatar da cewa harsasan da ta yi amfani da su ba irin na bindigarta ba ne.

Sun ce Nancy ta amshi garabasar manufofin inshorar rayuwa ana saura kwanaki kadan ta halaka mijinta.

Shawn Overstreet, mataimakin alkalin yankin, ya ce Nancy ce kadai mai burin halaka mijinta.

Sai dai lauyoyin da ke kare ta sun sanar da kotu cewa Nancy da mijinta su na ta shirin yin wata tafiya, inda su ka ce zarginta ake yi da laifin ba tabbaci aka samu ba.

Shaidun da aka gabatar wa kotu a ranar Laraba sun bayyana Nancy a matsayin wacce alamu su ka nuna cewa karara ta yi kisan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button