Idan Kunaso Mudaina shirin izzar so, to ga sharadi – Lawal Ahmad
Fitaccen jarumin nan masana’atar Kannywood Lawal ahmed wanda yake da suna a cikin shiri mai dogon zango da ya samu karbuwa Izzah so umar hashim.
Ya kawo wasu sharuda wanda duk yake son ya daina shiri mai dogon zango na izzah so, wasu na ganin wannan zance sam bai dace ya fito daga bakinsa, idan bazaku manta ba a kwanakin baya yayi irin wannan zance inda yake cewa duk wanda yake tambayar yaushe za’a gama shirin izzar so to baya kishin musulunci.
To shine yau ma jarumi yazo da wasu sharuda da ya wallafa sa shafinsa na sada zumunta facebook mai suna @lawanahmad yana mai cewa.
“Idan kuna so mu daina izzar so to sharadi zan fada muku.
1 kuje kusa a daina cin kasuwar kwari,da singa,da kasuwar rimi , da sabon gari kusa a rufe duk wani gidan mai da yake shayarda mai.
Kusa a dena zuwa makaranta ,kusa a rufe gidan gwamnati,ku sa a dena zuwa kowace kasuwa da duk sauran duk wani gari da ake yin kasuwanci.
Saboda haka anayine don kasuwanci nima inayin izzar so ne don kasuwanci.
Nagode”.– inji lawal Ahmad.
Hausaloaded ta samu tattara martanin mutane a karkashin wajen muhawara a kasa wnanan rubutun nasa.
@Auwal Ghali Auwal cewa yake : Hhhhhhh gaskiya ta bayyana yanzu dai,hakan na nufin ba don addini din akeyi ba kenan?
@sada suleiman usman cewa yake: Gaskiya Lawai ka ci kai!
@Gen sunusi cewa yake : Ka daina yi don addini kenan ka koma Kasuwanci…
@jeederh Aminu cewa take : Hahahaha Kuma da farko kace saboda musulunci kake yi,ya akayi yanzu Kuma ka dawo kace kasuwanci ne kakeyi kayi amai ka lashe kenan.
Don Allah karka fasa ka cigaba har mahadi ya bayyana