Yanzu – Yanzu: An Kori Babban Hafshan Soja Maciyin Amanar Tsaron Kasa Daga Aiki
Kotun sojoji (Court Martial) ta zartar da hukuncin korar Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki daga aiki sakamakon an sameshi da laifuka biyar ciki har da laifin satar kudi naira miliyon dari da talatin da biyar da dubu dari takwas (N135,800,000)
Janar Otiki shine tsohon kwamandan rundinar sojoji na 8 dake jihar Sokoto, an sameshi da laifin sace miliyoyin naira wanda aka ware domin tabbatar da tsaro a jihar Sokoto, yau Allah Ya kawo ajalin aikinsa da rundinar sojin Nigeria, an kwabe kakinsa.
Ana zarginsa da ya sace zunzurutun kudi naira Miliyon dari hudu ne, to amma an samu naira miliyon dari da talatin da biyar, korar wulakanci aka masa, sai da aka rage masa mukami daga Manjo Janar zuwa Birgediya Janar kafin nan sai aka koreshi, kuma an kwace kudaden da ya sace
Jama’a kunga irin wadanda suke cin amanar tsaron Nigeria, Allah Ya fara tona musu asiri, don haka mu dage da addu’ah
Yaa Allah Ka tona asirin duk wani maciyin amanar tsaron Nigeria Amin