Zuwa Ga Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Maigirma shugaban ‘kasa Muhammadu Buhari ni Datti Assalafiy na kasance daya daga cikin dunbin masoyanka, kullun burina a rayuwa shine na samu zaman sirri da kai domin baka tawa gudunmawa wajen tabbatar da tsaro a ‘kasarmu Nigeria
Ina matukar adawa da dukkan abinda zai taba gwamnatinka ya nuna gazawarka Yaa Maigirma shugaban ‘kasa, babban burina shine kaci nasara a shugabancinka
Amma bayan haka nazo maka da wata shawara wanda zai taimaka kwarai dagaske, duk da dai a tsorace nake saboda tsoron gujewa makircin maciya amana wanda basa kaunar a samu zaman lafiya a Nigeria, amma mawuyacin halin da ake ciki a Zamfara yasa zan sake bada tawa gudunmawa na shawara kamar haka:
A shekarar 2004 tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya kawo wani tsari a hukumar ‘yan sandan Nigeria na inganta tsaro daga ‘kasar Ingila, tsarin da a turance ake kira da (Community Policy) karkashin wannan ne nakeso na bada shawara
Maigirma shugaban ‘kasa, ka bada umarni wa rundinar sojin Nigeria ta nemo maka duk wani soja da ya fito daga jihohin Borno da Zamfara masu mukami daga Laftanar (Lieutenant) zuwa Manjo Janar (Major General), sannan kayi irin wannan umarni ga rundinar ‘yan sandan Nigeria ta nemo maka dukkan wani jami’in ‘dan sanda da ya fito daga jihohin Borno da Zamfara masu mukami daga Mataimakin sufurtendan ‘yan sanda (Assistant Superintendent of Police ASP) zuwa mukamin Kwamishinan ‘yan sanda (Assistant Inspector General of Police)
Maigirma shugaban ‘kasa idan aka nemo maka adadin wadannan jami’ai, sai kabi file dinsu ka karanci irin record da kowanne daga cikin jami’an yayi breaking a aikinsa na tsaro, wadanda sukafi jarunta da kwazo da basira da ilmi akan tsaro da rashin tsoro daga cikinsu zai ka zabesu, su kai adadin kananun hukumomi dake jihohin Borno da Zamfara, sai kasa a kira maka su, ka nemi zaman tattaunawar sirri tsakaninka da su
Idan ka tattauna dasu sai kace zaka basu wani national assignment, wadanda suka fito daga Borno zaka turasu Borno, wadanda suka fito daga Zamfara zaka turasu Zamfara, don haka su fadi dukkan abinda suke bukata na kayan yaki da ababen hawa, kuma su fada maka adadin kudi alawus na kula da walwalarsu da na kananun jami’ai wadanda zasuyi aiki karkashinsu da za’a bukata tun kafin a fara yakin, sannan ka basu damar da zasu karbi umarni kai tsaye daga gareka a filin yaki
Daga nan Maigirma shugaban ‘kasa sai kasa rundinar soji da na ‘yan sanda su nemo kananun jami’an tsaro wadanda suka fito daga jihohin Borno da Zamfara, sai kasa suyi aiki tare da wadancan manyan ofisoshi da ka zabo ka karanci record dinsu, kuma kowace karamar hukuma a tura jami’an tsaron da suka fito daga karamar hukumar tare da Kwamandansu ‘yan asalin karamar hukumar
Manufar hakan shine; jami’in tsaro da ya fito daga inda aka haifeshi zaifi kowa sanin sirrin yankinsa da harcen yaren kabila da akeyi a yankinsa, yana daya daga cikin abinda muka karanta a ilmin tsaro ba zaka iya cin nasaran tabbatar da tsaro a wani yanki ba matukar bakasan sirrin gurin ba, ba zaka dauko inyamuri daga jihar Abia sai ka turashi jihar Borno cikin kabilar Kanuri kace ya yaki Boko Haram har ya kai ga nasara ba, gaskiya haka bai taba faruwa ba a tarihin yakukuwan duniya.
Maigirma shugaban ‘kasa idan ka dabbaka wannan shawaran sai ka basu lokaci kace kana son kafin lokacin ya kare ba’a sake yin garkuwa da wani mutum a jihar Zamfara ba, ‘yan ta’adda basu sake kawo hari a ko’ina a jihar Borno ba, ka tabbata alawus dinsu mai kauri yana shiga akan lokaci, jami’an tsaron zasuyi aiki tukuru domin sun san al’ummarsu ne, jama’arsu zasu kare kuma mahaifarsu
A lokacin da umarni yazo wa jami’in tsaro, aka bashi umarni ya dauki bindiga da sauran kayan yaki yaje ya yaki ‘yan ta’adda, ‘yan fashi da makami ko kuma masu garkuwa da mutane, farkon abinda zai fara tunani a ransa shine mutuwa, zan iya rasa rayuwata, iyalai na fa? idan na mutu wa zai basu abinci? wa zai kula da karatunsu da tarbiyyah?, ina da muhalli? anya zanje a kasheni a banza rayuwar iyalaina ta tagayyara?
Don haka abune mai matukar wahala jami’in tsaron Nigeria yaje yayi abinda akeso matukar akwai wannan tunanin a ransa, saboda haka yana bukatar gwamnatin da yake yiwa aiki ta dauke masa dukkan nauyin abinda yake tunani a ransa idan aka kashe shi a fagen daga
Me ya kamata gwamnati tayi?
Gwamnati ta gabatar da wani tsari kamar haka:
Duk wanda aka turashi yaki da Boko Haram a Borno; duk wanda aka turashi yaki da masu sace mutane a Zamfara sai ace za’a basu “Life Insurance” duk wanda ya mutu gwamnati zata gina ma iyalansa gida a garinsa ko inda yake so, gwamnati zata dauki nauyin karatun yaransa a ‘kalla guda hudu tun daga matakin Primary har zuwa University su kammala.
Wannan shawarwari na gabatar dasu tun shekarar da ta gabata, bukata ce ta sa na sake kawo shawaran a yanzu.
Muna rokon Allah Ya isar mana da wannan shawara zuwa ga Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Amin