Akwai bukatar a kama Buhari – Gudaji, mahadi shehu cikin wata hira ta musamman


A wata hira ta musamman da gidan jaridar Dclhausa na yi da gudaji kazaure da kuma mahadi shehu akan Emefiele, idan baku manta a zaman da ankayi na kotu an tabbatar da Emefile ya mallaki asusun ajiya wato akawon guda 593 wanda duk a kasashen waje wannan babu shakka wannan mutum ya azurta kanshi da kanshi da kudin al’umma.
A cikin wannan hirar zaku irin yadda gudaji kazaure yake cewa daman tun can a baya sun nunawa duniya cewa tabbas tsohon gwamnan babban bankin Najeriya shine matsalar tattalin arziki Nijeriya kuma gashi nan abun ya fito fili anyi walkiya ta haska.


Ga kadan daga cikin hirar abinda honorabul gudaji kazaure ke fadi
“A akawun kadai a ingila an samu kusan fan din ingila miliyan dari biyar, wadannan kuɗi sune muke magana ya tara kuɗi ya rasa inda zaiyi da su, ya rasa inda zai kai su, daga sune ake rantawa Nijeriya kuɗin Nijeriya, daga sune ake baiwa inbesto “Investor” bashi , daga sune aka sanya ciki I &E window market, Wanda munka fito munkayi bayyani aka ƙi yadda – inji honorabul gudaji kazaure.
Sai nan inda mahadi shehu yake magana inda yake cewa.
“A kama buhari a kama duk wani ministocin buhari a rufe su yadda anka rufe emefiele , da yan uwan matar Buhari da makaraban buhari wadanda sun kaci gwamnati saboda wallahi mun san in bashi ankayi ba akwai ‘ya’yan mora da mowa, shi kadai za’a yi musan da gaske ake yi.
Buhari bai wuce darmu ba, ministoci basu wuce darmu ba, ga ministocin sa nan suna shagali suna taɓargaza da kuɗi suna fachaka da dukiya kuma ba wanda ya gaji kudi a cikin su duk yayan talakawa ne, munsan su sun sanmu wallahi- inji Mahadi shehu
Ga bidiyo.nan ku saurara domin jin cikakkiyar hirar nan tabbas Nijeriya anyi badaƙala sosai.
@dclhausa‘Akwai bukatar Tinubu ya kama Buhari’ – hira ta musamman da Mahadi Shehu da Gudaji Kazaure kan Emefiele
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






